Kungiyar masu masana’antu ta Nijeriya (MAN), ta ce karin kudin man fetur da aka yi zai iya haddasa tashin farashin kayayyaki.
Cikin wata sanarwa da shugaban MAN, Segun Ajayi-Kadir, ya fitar a ranar Laraba, ta ce matakin zai iya shafar kudaden shigar jama’a.
- Yusuf Tuggar: Hadin Gwiwar Sin Da Nijeriya Na Haifar Da Alfanu A Fannoni Da Dama
- Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Ta Fannin Sabbin Makamashi Ya Samar Da Mafita Ta Tabbatar Da Ci Gaba Mai Dorewa A Afirka
Ajayi-Kadir na mayar da martani ne kan karin farashin man fetur da aka yi a ranar Talata.
Kamfanin NNPC, ya kara farashin litar mai daga Naira 568 zuwa naira 855, matakin da ya haifar da ce-ce-ku-ce a fadin Nijeriya.
“Yayin da farashin mai ya tashi, kudaden da mutane ke kashewa zai karu a fannonin sufuri da makamashi, wanda hakan zai rage kudaden da suke samu.”
Ya kara da cewa lamarin zai fi shafar kananan masana’antu saboda kudaden da suke juyawa ba su taka kara sun karya ba.
Ko da yake, shugaban na MAN ya ce bai yi mamaki da karin kudin litar man ba, duba da cewa farashin mai ya tashi a kasuwar duniya.
“Farashin mai ya tashi a duniya. Matatun manmu ba sa aiki kuma muna shigo da mai ne,” in ji shi.