Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya ba da umarnin aika wa da motoci bas cikin Ilorin domin taimakawa masu zirga-zirga da suka shan wahala sakamakon tsadar kudin sufuri.
Karin farashin sufuri wanda ya samo asali daga tashin farashin mai, ya sa hanyar da a baya ake biya N500 yanzu ta koma N1,500, lamarin da ya sanya yawancin mazauna garin ba su iya biyan kudin mota.
- Zan Samar Wa Gwamnati Kudin Shiga Na Dala Biliyan 100 Ta Hanyar Fasaha – Hannatu Musawa
- Abokin Da Ke Iya Ba Ka Taimako A Lokacin Da Kake Bukata, Shi Ne Aboki Na Kwarai
Lamarin ya ƙara dagulewa lokacin da direbobin keke Napep suka shiga yajin aiki domin nuna rashin amincewa da farashin mai, wanda aka ce ya kai N1,200 kowace lita a Ilorin.
Domin rage wannan wahalar, gwamnan ya samar da motocin sufuri kyauta zuwa manyan wuraren tafiye-tafiye, don taimaka wa mazauna garin, har ma da waÉ—anda ke kan hanyarsu ta zuwa wuraren neman aikin yi.
Gwamna AbdulRazaq ya yi kira da a yi hakuri daga bangaren masu sufuri da al’umma baki daya yayin da gwamnati ke nazarin lamarin don nemo mafita. Ya amince da wahalar da karin farashin ke haifarwa, tare da tabbatar da cewa ana É—aukar matakan saukaka wadannan kalubale nan ba da jimawa ba.