Batun rasuwar uwa kwaya guda daya da ta kafa tarihi a Nijeriya da ma duniya baki daya, shi ne da ya fi kowane daukar hankali a cikin wannan makon.
Tun bayan bayyana rasuwar Hajiya Dada wanda ya shafe shekaru 102 a duniya al’amurra suka tsaya cak a Jihar Katsina , sannan aka shiga alhini da juyayin wannan baiwar Allah da aka yi shaida da cewa macce ce da ta sadaukar da rayuwar ta wajen yi addini da al’umma hidima.
- Barazanar Zanga-Zangar Kuncin Rayuwa Ta Girgiza Nijeriya
- An Cafke Wani Hedimasta Bisa Laifin Sayar Da Kayayyakin Makaranta A Kano
Tun bayan fitar labarin rasuwar ta, wanda dan autan ta, Alhaji Sukeiman Musa Yar’adua ya fitar jama’a da dama ke fadin abubuwan alheri game da ita da kuma ‘ya ‘yan da ta haifa.
Alal hakika za a dade ba a manta da Hajiya Dada ba, musamman saboda irin taimakon da ta yi wa al’umma wanda hakan tasa babu lokacin da babu mabukata a kofar gidan Matawalle Musa Yar’adua da ke cikin birnin Katsina
Mataimakin shugaban kasa Sanata Kashin Shettima ne ya jagoranci babar Tawaga wajen yi wa Hajiya Dada jana’iza a birnin Katsina.
An yi masa sallah a tsohon filin wasa da ke cikin Katsina da misalin karfe 1:550na rana wanda Sheikh Aminu Yammawa ya jagoranci yi mata Sallah tare da dubun dubatar al’umma duk da yanayi na ruwa.
Dangane da haka, wakilinmu a jihar Katsina El-Zaharadeen Umar ya yi bitar wasu abubuwa guda goma wanda ba kowa ya san su game da marigayiya inda fara nemo asalin sunanta wanda mahaifinta ya sanya mata.
Abu na farko da ya kamata mai karatu ya sani ahine, Tarihin Sunanta: Yau din muke kyautata zaton mai karatu ke jin labarin asalin sunan Dada wata Fatima Binta diyar Matawalle Sayyadi Gafai kuma matar matawalle Musa Yar’adua.
Haka kuma sai yau wata kila kake jin tarihin yadda ta sami sunan ta na Dada wanda duniya ta san ta da shi, da kuma sunan da mahaifinta ya sanya mata, wato Fatima Binta Sayyadi Gafai. Wannan suna na Dada suna ne da ‘ya ‘ya ke kiranta da shi na alkunya.
Mun san cewa a lokacin baya, ‘ya ‘ya ba sa iya kiran sunan mahaifiyar su, sai dai ka ji wasu na cewa Mama ko Baba ko Inna da kuma Gwaggo da sauran su, amma Ita ‘ya ‘yan ta suna kiran ta da Dada.
Sai abu na biyu, shi ne, Allah ya yi wa Hajiya Dada rasuwa a ranar Litinin 02/09/2024 a gidan ta da ke unguwar Yar’adua cikin birnin Katsina bayan ta shafe shekaru 102 a duniya.
Sannan an rufe marigayiyar ne a wani wuri na musamman da ake rufe manyan mutane da suka hada da sarakuna da Malamai da masu kudi da kuma masu mulki a cikin makabartar Dan Marna mai tarihi da ke cikin birnin Katsina
Haka kuma anan din dai aka rufe dukkanin ‘ya ‘yan ta guda biyar da suka rigata rasuwa: da suka hada da mijinta Matawalle Musa Yar’adua’ da Shehu Musa Yar’adua da Malam Umaru Musa Yar’adua da Hajiya Mairo Musa Yar’adua da Hajiya Hadiza Musa Yar’adua da kuma Alhaji Jafaru Musa Yar’adua
Abu na uku akan Marigayiya Dada shi ne, ita ce mata ta biyu a gidan Matawalle Musa Yar’adua kuma Allah ya azurtata da haihuwar ‘ya ‘ya guda tara a duniya maza shida mata uku.
Mazan sune kamar haka; Shehu Musa da Umaru Musa da Abdul’aziz Musa da Jafaru Musa da kuma dan auta Sukeiman Musa. Sai kuma matan akwai Maryam (Mairo) Musa da Hadiza Musa da Hafsat Musa da kuma Hajiya Habiba Musa Yar’adua
Allah ya yi wa guda biyar rasuwar Kamar yadda muka bayyana a farko, yanzu akwai mutum hudu suna raye, Alhaji Abdul’aziz Musa da Alhaji Suleiman Musa da kuma Hajiya Hadiza Musa tare da Hajiya Habiba Musa Yar’adua
Abu na hudu shi ne, da ya kamata mai karatu ya sani game da wannan baiwar Allah shi ne, Duniya ta shaida cewa Hajiya Dada ita ce mace uwa kwaya daya a Nijeriya da ta haifi shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa kuma take da jikoki da suke auren tsofaffin gwamnonin Nijeriya.
Misalin haka shi ne, Nafisa Umaru Yar’adua tana aure tsohon gwamnan Bauchi Malam Isah Yaguda, Maryam Umar Yar’adua tana auran tsohon gwamnan Katsina Ibrahim Shehu Shema, Hafsat Umaru Musa Yar’adua tana auran tsohon gwamnan Kebbi Sa’idu Nasamu Dakin Gari.
Sannan yanzu haka tana da da wanda yake Sanata a majalisar dattawan Nijeriya, Sanata Abdul’aziz Musa Yar’adua shugaban kwamitin sojojin Nijeriya.
Abu na biyar dangane da rayuwar marigayiya Dada shi ne, duk makusanta ta sun bayyana cewa Allah ya yi mata rashin yin magana wato dai bata cikin matan nan da ake cewa suna da yawan surutu, babu wanda ke shakkar haka.
Sai dai kuma sun kara da cewa idan har Allah ya sa ta yi magana, to lallai za a ji magana da ma’ana da hikima kuma darasin rayuwa wanda ake fatan cewa mata za su yi koyi da ita akan wannan dabi’a ta ta.
Abu na shida wanda ya kunshi tawakali da kuma sallamawa hukuncin ALLAH shi ne cikin baiwar da Allah ya yi Hajiya Dada Mahaifiyar tsohon shugaban kasa Umaru Musa Yar’adua, kafin rasuwar ta shi ne, sai dai Allah ta’ala ya nuna mata rasuwar ‘ya ‘yan ta fitattu a Nijeriya da kuma duniya baki daya har guda biyar
Daga cikin ‘ya ‘yan na ta wadanda suka rigata rasuwa; akwai marigayi tsohon mataimakin shugaban kasa Shehu Musa Yar’adua da tsohon shugaban kasa Malam Umaru Musa Yar’adua da Kuma Hajiya Maryam (Mairo) Musa Yar’adua da Hajiya Hadiza Musa Yar’adua (Dije) da kuma Alhaji Jafaru Musa Yar’adua
Wani abin birgewa shi ne yadda aka yi mata shaidar cewa bata taba tada hankalin ta ba dangane da rasuwar daya daga cikin ‘ya ‘yan nata ba. Tana mika al’amuranta zuwa ga Allah tare da sallamawa hukuncin Ubangiji.
Abu na bakwai da mai karatu zai sani game da rayuwar Hajiya Dada shi ne bayanin da dan autanta ya yi na cewa babu wani ciwo a tarihin rayuwar ta wanda ya hana ta sakewa musamman cututtukan zamani da ake fama da su.
Alhaji Sukeiman Musa Yar’adua ya kara da cewa mahaifiyar su, har Allah ya dauki ranta bata da ciwon zuciya hawan jini ko suga da dai sauran cututtukan zamani, sai dai tsofa da kuma shekaru.
Wannan ma wata baiwar ce da Allah ya yi mata, domin a irin wannan lokaci yana da wahala mutum ya yi shekaru irin na ta, amma ka ganshi lafiya lau baya da daya daga cikin cututtukan zamani.
Abu na takwas shi ne, Marigayiya Dada ita ce mata ta biyu a gidan Matawalle Musa Yar’adua kuma Allah ya azurtata da haihuwar ‘ya ‘ya guda tara a duniya maza shida nata uku.
Mazan sune kamar haka; Shehu Musa da Umaru Musa da Abdul’aziz Musa da Jafaru Musa da kuma dan auta Sukeiman Musa. Sai kuma matan akwai Maryam (Mairo) Musa da Hadiza Musa da Hafsat Musa da kuma Hajiya Habiba Musa Yar’adua
Allah ya yi wa guda biyar rasuwar Kamar yadda muka bayyana a farko, yanzu akwai mutum hudu suna raye, Alhaji Sukeiman Musa da kuma Hajiya Hadiza Musa tare da Hajiya Habiba Musa Yar’adua
Sai kuma abu na tara shi ne: Hajiya Dada ta kasance uwa guda daya ga duk wani dan siyasa da ake matukar girmamawa a Nijeriya.
Har ya zama wata al’ada ga ‘yan siyasa musamman lokacin yakin neman zabe, duk lokacin da wani babba ko jigo a siyasa ya ziyarci jihar Katsina sai ya kai mata gaisuwar ban girma irin ta uwa, mutum kowace jam’iyyar siyasa yake.
Abu na goma wanda shine na karshe a cikin jerin abubuwa guda goma da mu yi bitar su domin daukar darasi daga rayuwar marigayiya Dada sun hada da wasu abubuwa da ba a san su ba.
Hajiya Dada wato Fatima Binta Sayyadi Gafai ita ce mata ta biyu kamar muka bayyana sannan abikiyar zaman ta wanda ita ce mata ta uku a gidan Matawalle ita ma sunanta Dada kuma tare suke zaune a cikin gidan Matawalle kuma ita sunanta ba asali Fatima Binta.
Dukkan su ana ce masu Dada, wato Dada karama da kuma Dada babba, ita babbar ita ce take da manyan ‘ya ‘ya da suka shahara a duniya aka san su, sannan suka bautawa Nijeriya.
Daga karshe muna rokon Allah ta’ala ya jikan Hajiya Fatima Binta Sayyadi Gafai (Dada) da rahama ya kyautata makwancin ta yasa ta huta, ya baiwa iyalanta hakurin jure wannan baban rashi. Amin summa amin.