Duba da karatowar zabukan cikin gida da jam’iyyar PDP za ta fara gudanarwa a matakin mazabu a wasu jihohin wannan Kasa, cikinsu har da jihar Kano, ranar Asabar 7/09/2024, yana da kyau a dan yi wani tambihi game da zabukan. Sati biyu tsakani da gudanar da zabukan a matakin Mazabu, sai kuma a sake gudanar da wasu zabukan a matakin Kananan Hukumomi ran Asabar 21/10/2024. Sannan, sai ranar Asabar din 05/10/2024 ne za a gabatar da zabukan a matakin jihohi.
Wadannan zabuka dai, sun kasance zabuka ne na neman kujerun shugabancin jam’iyya, a tsakanin ‘yan jam’iyya, kamar yadda Kundin Tsarin Mulkin Kasa, da na Jam’iyya suka sahalewa masu sha’awar tsayawa, na, su tashi su nema, ba tare da nuna wani banbanci ba a tsakanin ‘yan jam’iyya. Ma’ana, babu’ya’yan-bora da na mowa, wajen fitowa neman kujerun!.
- Rikicin Masarautar Kano: NNPP Ta Nesanta Kanta Daga Umarnin Kwankwaso Ga Ƴan MajalisaÂ
- Zaben Kananan Hukumomin Kano: ‘Yan Takara 400 Na Tururuwar Kamun Kafa A NNPP
Saboda yanayi na son zuciya da ake zargin akasarin masu ruwa da tsaki na jam’iyya a wannan Kasa, sai aka wayigari maganar gudanar da zabukan cikin gida na jam’iyya cikin adalci da kyakkyawan yanayi na dimukradiyya, na neman zama wani tarihi ne a tsakanin jam’iyyun siyasarmu, musamman ma daga abubuwan da aka rika gani suna wakana karkashin wannan Jamhuriyar Siyasa ta Hudu (4th Republic) da muke ciki, wadda ta fara daga Shekarar 1999 zuwa yau (2024), na rashin gudanar da zabukan cikin gida bisa doron dokokin jam’iyyun, dokar zabe, da ma kundin tsarin mulki na Kasa, a cikin akasarin jam’iyyun a fadin Kasa. Ina kuma ga maganar babban zabe na Kasa (general elections), in har a matakin zabukan cikin gida na jam’iyya, (party primaries) za a zalunci dan-jam’iyya a tauye masa hakkinsa?.
Sannu a hankali, sai aka sauka daga kan gwadabe na gaskiya yayin gudanar da zabukan jam’iyya a Kasa, maganar mutum ya ci zabe, na hannun wasu katti daga masu ruwa da tsaki a jam’iyya. Sai ma aka daina maganar dantakarar da jama’a ke so, ko dantakarar da ya cancanta, wanda ya dauki lokaci yana yi wa jam’iyya da ‘ya’yan jam’iyya hidima, tun gabanin azo ranakun gudanar da zabukan. Wannan yanayi na-tur da aka rika yin kwalli da su tun a farko farkon wannan zangon dimukrradiyya na hudu, ya jaza haifar da kawo mummunar asarar rayuka da dukiyoyi a tsakanin al’umar wannan Kasa, musamman ma tsakanin magoya bayan jam’iyyun siyasa.
Cikin Shekarar 2002, an yi ta tafka asarar rayuka da dukiyoyi cikin da yawa daga zabukan cikin gida na jam’iyyu da aka gudanar, a wasu sakuna da lunguna na wannan Kasa, lamarin da wasu masana da sauran masharhanta suka fara tunanin cewa, lalacewar lamuran da ke wakana a lokacin, sakamakon son zuciya da dattawan jam’iyya ke nunawa a lokacin gabatar da irin wadancan zabuka, na iya zamowa silar tuntsurewar Kasar bakidaya. Mu dubi kalaman da tsohon shugaban Kungiyar Lauyoyi ta Kasa, Okocha, ya yi;
“…an wayigari ‘yan siyasa na kashe kansu da kansu, yayinda suka tasamma gudanar da zabukan cikin gida na jam’iyya… lokaci ya yi da ya kamata ‘yan siyasa su farka ne daga irin dogon barcin da suka sami kansu ciki. Ina tsoron ka da su zama sune silar matsalar wannan Kasa ta Najeriya…”.
(Tell, 16th September, 2002 & Anwar, 2014).
Kakaben ‘yantakara Da Karyewar PDP, 2002, 2011
Wasu masharhanta na da tunanin cewa, batun kakaba ‘yantakarar da ba su ne hakikanin zabin ‘yan jam’iyya ba, ya taimaka ainun wajen wargajewar jam’iyyar ta PDP cikin wannan Jamhuriyar Siyasa ta Hudu da muke ciki.
A Jihar Ogun
An sami mummunan rashin fahimtar juna game da batun ‘yantakara, tsakanin tsohon shugaban Kasa Obasanjo da kuma gwamna Gbenga Daniel. Wani abin takaicin ma shi ne, a lokacin wannan dambarwar yi wa ‘yan jam’iyya kakabe, Obasanjon ne shugaban Kwamitin Amintattu na jam’iyyar PDP a duk fadin Kasa. Ke nan, batun da aka faro a farkon wannan rubutu cewa, manyan masu ruwa da tsaki na jam’iyyu ne ke shake jam’iyyar, ko suke gaza yi wa ‘yantakara adalci lokacin gudanar da zabuka gaskiya ne!. Sai dai, a karshen lamari, za a ga cewa, hadamar da dattijan ke nunawa, na kassarar jam’iyya ne dungurungum.
(Source, 7th February, 2011: 16-17-18-19-20, 22-23).
A Jihar Enugu
A ita ma jihar ta Enugu, rikicin dankarawa ‘yan jam’iyya dantakara ne ya barke, a tsakanin gwamnan jihar, Sulliban Chime, da tsohon shugaban jam’iyyar PDP ta Kasa, Okwuesileze Nwodo. A sanadiyyar rikicin na wadannan manyan giwaye biyu, jam’iyyar ta dare ne zuwa gida biyu. Ga bangaren gwamna. Sannan, ga bangaren tsohon shugaban jam’iyyar na Kasa, wanda tsohon shugaban Majalisar Dattijai ta Kasa, Ken Nnamani, ke marawa baya. Ba karamin lahani wannan dambarwar ta ci gaba da yi wa jam’iyyar PDP ba a wancan lokaci.
A Jihohin Kano, Oyo, Imo, Anambra, Lagos
A cikin wadannan jihohi na sama da ma wasunsu, duka cikin Shekarar ta 2011 an ta samun korafe-korafe ne game da wasu shugabanni da jagororin jam’iyyar a matakin jiha, shiyya da matakin Kasa, a yunkurinsu na dankarawa ‘yan jam’iyya wasu ‘yantakara na daban, wadanda ba sune zabinsu ba.
(Ibid).
Da Sauran Tsalle A Jihar Kano, 2024
Yanzu haka ma a jihar Kano, akwai wata wutar rikici kwance na ruruwa, game da batun wane ne zai zama shi ne halastaccen shugaban jam’iyyar a matakin jiha? Ba sai an kama suna ba, yanzu haka cikin manyan dattijan jam’iyyar a matakin jiha da shiyya, da ma matakin Kasa bakidaya, an tabbatar da rabuwar kansu gida biyu. Kowannensu na da nasa dantakara kunshe cikin jaka. Na’am, manyan jam’iyya ko dattijai, na da cikakken ‘yanci cikin zuciyarsu da baiyane cewa, wane shi ne zabina, shi ne nawa dantakara. To shin, suna da ‘yancin cewa, lallai wannan dantakara nasu shi ne wanda dole za a zaba?. Ko kusa, ba su da irin wannan ‘yanci a dimukradiyance! Babu makawa, wajibi ne abar hukuncin tabbatar da dantakara a hannun akasarin ‘yan jam’iyya a ranakun gudanar da zabukan. Sabanin haka, abinda ya ci doma kuwa, ko kusa, ba shi barin awai!.
Yanzu haka dai cikin Kanon, da dama daga wadanda na sami damar tattaunawa da su, babban abinda suke kira a kai, bai wuce wasu abubuwa uku (3) ba;
i- Suna jan-hankali, ta hanyar hakaitar da irin matsalolin da suka durkusar da jam’iyyar tasu ta PDP tun a baya, wato dankaren dantakara, tare da neman, lallai ne abar wa dimukrradiyya damar yin kanta. Ma’ana, duk dantakarar da ya fi kowa samun rinjayen halastattun kuri’u, to shi ne ya ci zabe. Da sharadin, ba a tursasa mutane zabarsa ba.
ii- Da yawan ‘yan PDPn Kanon, na yin kira ga dattijai da kuma jagororin jam’iyyar a Kano, na, su hada-kansu wuriguda, tare da samar da ingantaccen zabe, tare da kaucewa duk wani yunkuri, na cewa, lallai lallai sai an zabi wane. Bukatar ingantattun zabukan kuwa, su faro tun daga matakin mazabu ne, har zuwa ga matakin zaben jiha.
iii- Kukan ‘yan jam’iyyar PDPn Kanon na karshe shi ne, idan jagororin jam’iyyar a Kano suka gaza hada-kansu game da batun zabukan, to fa wajibi ne masu ruwa da tsaki a matakin Kasa na jam’iyyar, mutane irinsu Sule Lamido da Wazirin Adamawa da sauransu, su shigo ciki, don kaucewa maimaicin haife Da Maras Idanu a PDPn Kano!!!.
Dakiki Ne Ke Maimaita Aji
Da yawan masharhanta na jan-hankalin jam’iyyar ta PDP da ma waninta cewa, su yi duk mai yiwuwa, wajen kaucewa siyasar dauki-dora, musamman ma a jihar Kano, Kanon da ta tsotsi nonon siyasar-naki, daga kirjin marigayi Malam Aminu Kano, marigayi Lawan Dambazau, marigayi Mudi Sipikin da ire-irensu.
Zai zama tamkar dakikanci ne jam’iyyar PDP ta tasamma maimaita irin waccan halaiyar, ta dankarwa jama’a dantakarar da ba shi ne zabinsu ba. Duba da irin haihuwar guzuma da jam’iyyar ta rika yi, tun daga Shekarar 2011, har zuwa lokacin da aka kammala jana’izarta cikin Shekarar 2015 a duk fadin Kasa.
Gani Ga Wane…
Babu shakka a Kano, akwai darussa iri daban-daban wadanda jam’iyyar ta PDP za ta iya yin amfani da su, wajen kaucewa yanayi na haihuwar guzuma, a batun likawa ‘yan jam’iyya dantakarar da ba shi ne zabinsu ba. Cikin Shekarar 2011, an tabbatar da cewa, kafewar da Malam Ibrahim Shekarau ya yi cewa, tilas dole sai an zabi Malam Saluhu Sagir Takai a matsayin dantakarar kujerar gwamna, karkashin jam’iyyar ANPP, shi ne yakai keyar Malam da Takai Kasa!.
Jam’iyyar CPC ma cikin Shekarar 2011, dagewar da jagororin jam’iyyar suka yi a matakin Kasa cewa, Janar Jafaru Isa (rtd.) ne dantakararsu, shi ne babban abinda ya buga Buba Galadima da Buhari da Kasa a Kano. Bugu da kari, yunkurin dankara dantakara cikin jam’iyyar PDP a Kano, cikin Shekarar 2011, shi ne babban silar raba auren siyasa tsakanin Kwankwaso da Jonathan.
Maganar dantakarar kujerar shugabancin jam’iyya da dantakara na kujerar mulki duka abuguda ne. Kowannensu na neman kuru’un mutane mafiya rinjaye ne, don kai wa ga nasarar lashe zabe, koko a yi maslaha. Kowannensu, na son ayi masa adalci ne. Kowannensu, na da hakkin a bar shi ya nemi kujerar da yake da muradin tsayawa a zabe shi. In kunne ya ji…!