ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, June 15, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Zaben Kananan Hukumomin Kano: ‘Yan Takara 400 Na Tururuwar Kamun Kafa A NNPP

by Abdullahi Muh'd Sheka
2 years ago
Kano

A yayin da zaben shugabannin kananan hukumomi da kansiloli a Jihar Kano ke kara karatowa, ‘yan takara sai karuwa suke yi, musamman ma a jam’iyya mai mulki ta NNPP, wanda yanzu haka akwai masu shawa’ar shugabancin kananan hukumomin 44 da suka haura mutum 400, inda kusan kowacce karamar hukuma ke da akallah masu zawarcin kujerar sama da mutum 20.

Wannan ambaliyar ‘yan takara a karkashin tutar jam’iyya mai mulki baya rasa nasa ba da irin salon jagoran darikar Kwankwasiyya, Rabiu Masu Kwankwaso wanda a baya a lokacin mulkinsa ya bayyana cewa, ‘kazarsa ta yi kwai 44 kuma ba za ta yi baragurbi ba’, hakan ta sa wasu ke ganin irin wannan za a maimaita a kakar zaben mai zuwa.

  • Laifukan Zabe Barazana Ne Ga Samun Sahihan Zabuka A Nijeriya – INEC
  • Hukumar Kashe Gobara Ta Ceto Wata Mata Da ‘Ya’yanta Biyu Bayan Ruftawar Gini A Kano

Sai dai kuma a wannan karo ana ganin kila a fuskanci turjiya, domin tun yanzu an fara jin bullar wasu ‘yan takara da ake kira da ‘yan takarar Miller da kuma wasu da ake wa lakabi da Abba tsaya da kafarka.

ADVERTISEMENT

Wannan kuma baya rasa nasaba da irin dabaibayin da jagoran Kwankwasiyyar ya yi wa Gwamnatin Abba Kabir Yusuf. Wadda wasu ke ganin gwamnan ba shi da wani katabus kan abin da ya shafi tsayar da ‘yan takara, domin hakan ta faru a baya a lokacin nada kantomin riko, wanda Gwamna Abba na kasar Saudiyya aka yi kuma aka gama.

Wata majiya ta tsegunta wa Jaridar LEADERSHIP HAUSA cewa, ana zargin ware wasu mutane uku da ake ganin su ne za su yi uwa kuma su yi makarbiya wajen tsayar da dukkanin ‘yan takara, musamman a wuraren da aka kasa samun maslaha.

LABARAI MASU NASABA

Atiku Ya Soki Shirin Bashin Naira Tiriliyan 4 Na Bangaren Wutar Lantarki

2027: ADC Ta Fara Sulhunta Mambobinta Da Ba Su Gamsu Da Zaɓen Fidda Gwani Ba A Kaduna

Haka kuma batun maslahar ma ana ginin maslaha ce ko a sa a baka. Domin an fara jin wasu na fara tanadar kudin na gani ina so domin mika wa masu ido da kwalli.

Amma kuma dole sai jam’iyyar NNPP ta yi karatun ta nutsu, domin jam’iyyun adawa, musamman jam’iyyar APC da takwararta ta PDP na ganin sahun gwamanti mai mulki a Kano ya shiga rafkanuwa, musamman idan aka yi la’akari da badakalar kudade da ke kara bayyana wadda ake zargin wasu na kusa da gwamnati da hannu a ciki dumu-dumu.

Wadannan matsaloli da su ne jam’iyyun adawa za su matsa a lokacin yakin neman zabe, sai kuma batun masarautu da aka mayar da sarakuna masu daraja ta biyu a birnin na Kano, ita ma wannan matsala za ta yi tasiri, musamman a yankunan da suka fara amfanar sabbin masarautun wadanda bayan shigowar gwamnati NNPP ta rushe su tare da mayar da su masu daraja ta biyu, wanda hakan ya yi matukar fusata mazauna wadannan yankuna.

Haka ma batun kudaden tsayawa takara da hukumar zabe mai zaman kanta a Kano ta ayyana, na nuni da wani shiri na hana duk wani mai karamin karfi ko wadanda ba su da gwamnati samun damar shiga takarar a dama da su sakamakon tsawwala kudaden takarar, inda aka a je naira miliyon 10 a matsayin kudin na gani ina so ga duk mai bukatar tsayawa takarar kujerar shugabancin karamar hukuma zai biya, yayin da kansila kuma zai biya naira miliyon 5 lakadan.

Wasu na ganin jam’iyyar NNPP za ta yi amfani da karfin ikon da ke hannunta wajen saya wa duk wadanda suka tsayar takara fom, yayin da sauran jam’yyun da ba su da mulki ana ganin an takura musu.

Wannan ta sa yanzu haka wasu gamayyar kungiyoyi ke shirin gurfanar da hukumar zaben mai zaman kanta ta Jihar Kano a gaban kotu domin bin ba’asin tsawwala kudazen takarar.

Koma dai me ake ciki ‘yan makonni kadan suka rage domin gudanar da zaben fid da gwani, wanda sakamakonsa ne zai nuna wa saura jam’iyyun makomarsu da kuma ‘yan takara da ba su da uwa a gindin murhun jam’iyya mai mulki, wanda ake kyautata zaton za a yi bari wanda jam’iyyun adawa za su daka wasoson su.

Kano
Abdullahi Muh'd Sheka
+ postsBio
  • Abdullahi Muh'd Sheka
    https://hausa.leadership.ng/author/abdullahi-muhd-sheka/
    Sakamakon Matsin Lambar Jami’an Tsaro, ‘Yan Ta’adda Na Fuskantar Ƙarancin Abinci
  • Abdullahi Muh'd Sheka
    https://hausa.leadership.ng/author/abdullahi-muhd-sheka/
    Kisan Gillar Mutum 7 A Kano: Sarakuna Da Malamai Da Iyaye Sun Nemi A Gaggauta Yanke Wa Waɗanda Ake Zargi Hukunci
  • Abdullahi Muh'd Sheka
    https://hausa.leadership.ng/author/abdullahi-muhd-sheka/
    MACBAN Ta Nemi Amurka Ta Cire Sunanta Daga Jerin Waɗanda Ta Ƙaƙabawa Takunkumi
  • Abdullahi Muh'd Sheka
    https://hausa.leadership.ng/author/abdullahi-muhd-sheka/
    Faɗace-Faɗacen Daba Da Ƙwacen Waya A Kano Ya Ɗauki Sabon Salo

MASU ALAKA

Atiku Ya Soki Shirin Bashin Naira Tiriliyan 4 Na Bangaren Wutar Lantarki
Labarai

Atiku Ya Soki Shirin Bashin Naira Tiriliyan 4 Na Bangaren Wutar Lantarki

June 14, 2026
ADC Ta Fara Sayar Da Fom Din Takara Kafin Babban Taron Jam’iyya
Siyasa

2027: ADC Ta Fara Sulhunta Mambobinta Da Ba Su Gamsu Da Zaɓen Fidda Gwani Ba A Kaduna

June 9, 2026
A Ƙarshe Jamilu Gwamna Ya Samu Babbar Dama Ta Yin Takara
Siyasa

A Ƙarshe Jamilu Gwamna Ya Samu Babbar Dama Ta Yin Takara

June 8, 2026
Next Post
Wainar Da Aka Toya A Taron ‘Yan Jarida Na Hausa A Nijar

Wainar Da Aka Toya A Taron ‘Yan Jarida Na Hausa A Nijar

LABARAI MASU NASABA

Farashin Mai Ya Fadi Rigis Bayan Amurka Da Iran Sun Sasanta Kan Mashigar Hormuz

Farashin Mai Ya Fadi Rigis Bayan Amurka Da Iran Sun Sasanta Kan Mashigar Hormuz

June 15, 2026
An Daure Ɗan Gidan Gimbiyar Masarautar Norway Shekara 4 Kan Laifin Fyaɗe

An Daure Ɗan Gidan Gimbiyar Masarautar Norway Shekara 4 Kan Laifin Fyaɗe

June 15, 2026
An Yi Wa Mata 600 Gwajin Cutar Sankarar Mama, An Yi Wa 50 Tiyata A Katsina

An Yi Wa Mata 600 Gwajin Cutar Sankarar Mama, An Yi Wa 50 Tiyata A Katsina

June 15, 2026
Ƴansanda Sun Kashe Ƴan Bindiga Uku Yayin Zazzafar Musayar Wuta

Ƴansanda Sun Kashe Ƴan Bindiga Uku Yayin Zazzafar Musayar Wuta

June 15, 2026
Jamus Ta Sake Yi Wa Abokiyar Karawarta Ruwan Ƙwallaye 7 A Gasar Kofin Duniya

Jamus Ta Sake Yi Wa Abokiyar Karawarta Ruwan Ƙwallaye 7 A Gasar Kofin Duniya

June 14, 2026
Ministoci Da Gwamnoni Za a Koma Kai Wa Hari Nan Gaba – Buratai

Ministoci Da Gwamnoni Za a Koma Kai Wa Hari Nan Gaba – Buratai

June 14, 2026
Jigilar Hajoji Ta Jiragen Kasa Na Gudana Bisa Daidaito A Kasar Sin

Jigilar Hajoji Ta Jiragen Kasa Na Gudana Bisa Daidaito A Kasar Sin

June 14, 2026
Atiku Ya Soki Shirin Bashin Naira Tiriliyan 4 Na Bangaren Wutar Lantarki

Atiku Ya Soki Shirin Bashin Naira Tiriliyan 4 Na Bangaren Wutar Lantarki

June 14, 2026
An Bude Bikin Fina-Finan Kasa Da Kasa Na Shanghai Karo Na 28

An Bude Bikin Fina-Finan Kasa Da Kasa Na Shanghai Karo Na 28

June 14, 2026
Ododo Ya Kai Ziyara Sansanin Horar Dakarun Tsaro Daji A Kogi

Ododo Ya Kai Ziyara Sansanin Horar Dakarun Tsaro Daji A Kogi

June 14, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.