Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid mai rike da kofin gasar zakarun Turai ta Champions za ta fafata da Liberpool a zagayen farko na gasar da aka sauya wa fasali ta 2024-25 a sabon tsarin da hukumar ta nahiyar turai ta fitar.
A satin da ya gabata ne aka raba jadawalin sabon tsarin gasar da za a fara amfani da shi a kakar wasa ta bana mai kungiyoyi 36 kuma sauran kungiyoyin da Real Madrid za ta fafata da su a zagayen su ne Dortmund, AC Milan, Atalanta, Salzburg, Lille, Stuttgart, Brest.
- Mutum Miliyan 7.9 Da Ta’addanci Ya Tagayyara A Jihohi 3 Na Bukatar Agaji – UNOCHA
- Champions League: Real Madrid Ta Zama Zakara Bayan Doke Dortmund
Muhimmin sauyi da kwamitin zartarwa na UEFA ya sanar shi ne ficewa daga tsarin matakin rukuni da ake yi a baya, inda a yanzu kowace kungiya za ta buga wasa takwas – hudu a gida, hudu a waje, amma ba gida da waje ba.
A baya matakin rukuni na gasar zakarun Turai ya kunshi kungiyoyi 32, da ake rabawa cikin rukuni takwas, inda kowanne rukuni ke kunshe da kungiyoyi hudu, sannan sauran wasannin da za su fi zafi a zageyn sun hada da wanda PSG za ta kara da kungiyoyin Manchester City, Bayern Munich, Atletico Madrid, Arsenal.
Yadda jadawalin sabon tsarin zai kasance
A yanzu kungiyoyi 36 ne za su shiga gasar, mai tsarin lig daya, inda duka kungiyoyin za su kasance a teburi daya domin tantance kungiyoyin da za su fafata da juna, da farko an rarraba su a cikin tukwane hudu bisa matsayin kowace kungiya.
An yi amfani da wata manhaja da UEFA ta samar domin fitar da kungiyoyin da kowacce kungiya za ta fafata da su kuma a matakin farko babu kungiyar da za ta fafata da abokiyar hamayyarta da suka fito daga kasa daya. Hakan na nufin kowace kungiya za ta kara da kungiyoyi biyu daga kowace tukunya cikin hudu.
Wasannin Man City
Bayern Munich (a gida) Borussia Dortmund (a waje) Atalanta ( a gida) Benfica (a waje) Young Boys (a gida) Red Star Belgrade (a waje) Brest (h) Monaco (a)
Wasannin Arsenal
PSG (a gida) Inter Milan (a waje) Shakhtar Donestsk (a gida) Atalanta (a waje) Dinamo Zagreb (a gida) Sporting CP (a waje) Monaco (a gida) Girona (a waje)
Wasannin Bercelona
Bayern Munich (a gida) Borussia Dortmund (a waje) Atalanta (a gida) Benfica (a waje)
Young Boys (a gida) Red Star Belgrade (a waje) Brest (a gida) Monaco (a waje)
Sannan idan aka kammala wasannin zagayen farko kungiyoyin za su kasance a teburi daya wato daga na daya zuwa na 36 inda daga nan ne kuma sai kungiyoyi takwas na saman teburi su tsallaka kai-tsaye zuwa zagayen ‘yan 16, yayin da daga kan kungiya ta tara zuwa 24 za su yi wasan neman gurbi (gida da waje), don kaiwa zagayen ‘yan 16.
Su kuwa wadanda suka kare a matsayi na 25 zuwa 36, an fitar da su daga gasar kenan, kuma ba za su samu damar shiga gasar Europa League ba, kamar yadda ake yi a baya hakan yana nufin an daina tafiya gasar Europa daga kofin zakarun Turai.
Daga kan matakin zagayen ‘yan 16 kuma sai a ci gaba da yadda aka saba gudanar da ita a baya – wato a kai matakin dab da kusa da na karshe, da matakin kusa da karshe, har zuwa wasan karshe, wanda za a yi a Birnin Munich na kasar Jamus, sannan yawan wasannin da za a fafata a sabon tsarin zai karu daga 125 zuwa 189.
Kowace kungiya za ta yi wasa takwas mafi karanci maimakon shida da kungiyoyin da ake fitarwa daga gasar tun a rukuni ke samun damar yi a baya, sannan za a gudanar da wasan zagayen farko har zuwa karshen watan Janairu, maimakon a baya da yake karewa kafin bikin Kirsimeti.
Wadanne kungiyoyi ne za su buga gasar a bana?
Tukunyar farko: Real Madrid (Spa), Man City (Eng), Bayern Munich (Ger), Paris St-Germain (Fra), Liberpool (Eng), Inter Milan (Ita), Dortmund (Ger), Leipzig (Ger), Barcelona (Spa) Tukunya ta biyu: Bayer Leberkusen (Ger), Atletico Madrid (Spa), Atalanta (Ita), Jubentus (Ita), Benfica (Por), Arsenal (Eng), Club Brugge (Bel),
Shakhtar Donetsk (Ukr), AC Milan (Ita).
Tukunya ta uku: Feyenoord (Ned), Sporting Lisbon (Por), PSB Eindhoben (Ned), Dinamo Zagreb (Cro), Salzburg (Aus), Lille (Fra), Red Star
Belgrade (Ser), Young Boys (Sui), Celtic (Sco).
Tukunya ta hudu: Sloban Bratislaba (Ska), Monaco (Fra), Sparta Prague (Cze), Aston Billa (Eng), Bologna (Ita), Girona (Spa), Stuttgart (Ger), Sturm Graz (Aus), Brest (Fra)