• English
  • Business News
Tuesday, October 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Rushewar Gine-gine Ta Yi Sanadiyar Rasuwar Mutane Fiye Da 90 A Shekara Daya

by Idris Aliyu Daudawa
1 year ago
Rushewa

Lamurran rushewar gine- gine da suka faru a ‘yan shekarun da suka gabata da akwai bukatar lalle a tsakanin masu ruwa da tsaki, wadanda su ya dace su yi wani abu dangane da nagarta ko sahihancin ayyukan da aka yi wadanda suka shafi gine- ginen da ake yi a fadin tarayyar Nijeriya.

Daga Arewaci zuwa kudancin Nijeriys an samu rushewar gine-gine masu yawa a cikin shekara daya da rabi, inda aka samu  asarar rasuwar mutane da kuma daruruwan mutane wadanda suka samu raunuka.

  • Zargin Aringizon Kasafin 2024: Majalisa Ta Jingine Sanata Ningi Bayan Ya Farke Laya
  • Rikicin Masarautar Kano: Sarki Bayero Ya Ƙaddamar Da Sabunta Ginin Fadar Nassarawa

Ga al’ummar Nijeriya suna yi ma lamarin rushewar gine- gine a Nijeriya a matsayin wani abu ne wanda ba wanda ya san lokacin da za a kawo karshen shi.

Bayan bilyoyin Nairorin da aka yi asara bugu da kari har rasa rayukan mutane saboda rushewar gine- ginen da ba a taba tsammani ba, wanda mutane da yawa musamman Leburori suke makalewa, yayin da kuma wasu ana barsu babu yadda za’ a iya yi dangane da halin da suke ciki.

Masu sharhi na Jaridar mako ta Weekend Trust sun nuna cewa a shekarar 2023 mutane, 49 ne suka mutu a sanadiyar rushewar gine- gine da suka faru fiye da sau 35.

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Gombe Ta Ceto Yara 59 Da Aka Yi Safararsu

An Shiga Ruɗani A Borno Bayan Budurwa Ta Kashe Kanta Saboda Auren Dole

Amma kuma a shekarar 2024 kadai matsalolin da aka samu sanadiyar rushewar gidaje kadai ya karu zuwa 42, wato ‘yan kwanaki kadan bayan rabin watannin shekarar.

Matsalar rushewar gine- gine ta shafi har gine- ginen da ba a kammala ba tare da wadanda suka tsufa suma suna fadi, sun kuma shafi wuraren da ake yin al’amuran da suka shafi addini, har ma da sauran gine- gine suma fadi suke yi.

A shekarar 2023 mutane 203 ne suka samu raunuka  a irin nau’ukan rushewar gine- gine,a wani aji a sansanin ‘yan gudujn hijira da ke Munguno a Jihar Borno  inda mutane 201 abin ya rutsa da su,inda mutum 6 suka mutu uku kuma suka samu raunuka.

Duk a shekarar mutane hudu sun mutu a gidajen ma’aikata gona a unguwar Mgbemena cikin Enugu lokacin da gini  ya rushe. Hakanan ma gida mai hawa daya ya fadi a Egbu Umuenem, Otolo Nnewi, a karamar hukumar Nnewai ta Arewa JIhar Anambra inda aka samu mutane uku suka mutu.

A Legas hedikwatar kasuwanci ta kasa sai ta kasance tamkar wani wuri ne daya saba da rushewar gine- gine an samu nau’oin lamarin inda 10 daga cikin 35 da suka faru a shekarar data gabata ta 2023.Gida mai dakuna 500 da ke a rukunin gidaje na Agboye Estate, Oduntan akan hanyar Ketu-Ikos inda mutane 2 suka samu raunuka, yayin da wani gida mai hawa biyu ya ruguje a namba 34, kan titin Oloto ,daura da titin Borno, Ebute Metta, Oyingbo,inda mutum daya ya mutu kafin  karshen shekarar.

Duk dai a shekarar data gabata Jihar Anambra ita ma ta samu ruguwar gine- gine a sashen kudu maso gabashin Jihar. Gida mai dakuna 20 ya ruguje duk da yake ba a samu wanda ya samu rauni ba 20.

Babban birnin tarayya Abuja shi ma ba a barshi a baya ba a lamarin rugujewar gidaje.Gida mai hawa biyu a rushe a  layin 6th Abenue Gwarinpa cikin watan Fabrairu inda mutane biyu suka mutu 60 suka samu raunuka.

Yayin da kungiyar kula da al’amuran injiniyoyi ta kasa (COREN) wadda ke kulawa da al’amuran da suka shafi ayyukan injiniya, sun bayyana cewa, Nijeriya ta hadu da lamarin rugujewar gidaje  22 tsakanin watannin Janairu da Yuli na 2024, an samu bayanai kamar yadda dakin karatu na Daily Trust ya nuna mutane 42 ne suka mutum a lamuraran da suka rushewar gidaje  zuwa ranar 15 ga watan Yuli.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwamnatin Gombe Ta Ceto Yara 59 Da Aka Yi Safararsu
Manyan Labarai

Gwamnatin Gombe Ta Ceto Yara 59 Da Aka Yi Safararsu

October 21, 2025
An Shiga Ruɗani A Borno Bayan Budurwa Ta Kashe Kanta Saboda Auren Dole
Labarai

An Shiga Ruɗani A Borno Bayan Budurwa Ta Kashe Kanta Saboda Auren Dole

October 20, 2025
Ƙungiyar Ƙwadago Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Ta Sasanta Da ASUU
Labarai

Ƙungiyar Ƙwadago Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Ta Sasanta Da ASUU

October 20, 2025
Next Post
’Yan Kasuwa Daga Kasashe Da Yankuna 119 Sun Halarci CIFIT Karo Na 24 

’Yan Kasuwa Daga Kasashe Da Yankuna 119 Sun Halarci CIFIT Karo Na 24 

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Gombe Ta Ceto Yara 59 Da Aka Yi Safararsu

Gwamnatin Gombe Ta Ceto Yara 59 Da Aka Yi Safararsu

October 21, 2025
Matsayar Kasar Sin A Bayyane Take Dangane Da Batutuwan Cinikayya Da Tsagin Amurka

Matsayar Kasar Sin A Bayyane Take Dangane Da Batutuwan Cinikayya Da Tsagin Amurka

October 20, 2025
An Shiga Ruɗani A Borno Bayan Budurwa Ta Kashe Kanta Saboda Auren Dole

An Shiga Ruɗani A Borno Bayan Budurwa Ta Kashe Kanta Saboda Auren Dole

October 20, 2025
Sin Ta Kara Wasu Wurare 22 Cikin Yankunan Dausayi Masu Matukar Muhimmanci A Kasar

Sin Ta Kara Wasu Wurare 22 Cikin Yankunan Dausayi Masu Matukar Muhimmanci A Kasar

October 20, 2025
Tinubu Ya Taya Kwankwaso Murnar Ranar Haihuwa, Ya Jaddada Abotarsu

Tinubu Ya Taya Kwankwaso Murnar Ranar Haihuwa, Ya Jaddada Abotarsu

October 20, 2025
Sin Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta Tsakanin Pakistan Da Afghanistan

Sin Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta Tsakanin Pakistan Da Afghanistan

October 20, 2025
Ƙungiyar Ƙwadago Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Ta Sasanta Da ASUU

Ƙungiyar Ƙwadago Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Ta Sasanta Da ASUU

October 20, 2025
Gina Kasar Sin Ta Dijital Na Kara Gaba Zuwa Sabon Matakin Amfani Da Basira

Gina Kasar Sin Ta Dijital Na Kara Gaba Zuwa Sabon Matakin Amfani Da Basira

October 20, 2025
Mutane 3,433 Sun Rasa Rayukansu A Haɗurra 6,858 A Cikin Watanni Tara

Mutane 3,433 Sun Rasa Rayukansu A Haɗurra 6,858 A Cikin Watanni Tara

October 20, 2025
An Gudanar Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Tsakiyar JKS Na 20 A Beijing

An Gudanar Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Tsakiyar JKS Na 20 A Beijing

October 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.