Gwamnatin jihar Kano ta dage ranar da za a koma makarantun firamare da na Sakandire na shekarar 2024/2025 har zuwa wani lokaci.
Gwamnati ta ba da dalilai na gaggawa ne wanda ba ta ayyana su ba a matsayin abubuwan da suka tilasta dage komawa makarantun.
- Yadda Sabon Tsarin Kofin Zakarun Turai Zai Kasance
- Gwamnonin Arewa Sun Sha Sabuwar Damara A Kan Matsalolin Yankin
Matakin dai ya biyo bayan wani mataki makamancin haka da gwamnatin jihar Edo ta dauka, wanda ta dage komawa makarantun saboda tashin farashin man fetur da kuma kalubalen da iyaye da masu kula da su ke fuskanta.
Balarabe Kiru, Daraktan wayar da kan jama’a a ma’aikatun ilimi ta jihar Kano ne ya sanar da dage komawa makarantun a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar.
Ya bayyana cewa, kwamishinan ilimi, Umar Doguwa zai sanar da sabon ranar da za a koma makarantun nan ba da jimawa ba.