Kwamitin yaki da Ambaliyar ruwa na jihar Kaduna ya bayyana yin gine-gine ba tare da izini ba da kuma zubar da shara a magudanun ruwa a matsayin manya daga cikin abubuwan da ke haifar da yawaitar ambaliya da sauran bala’o’in muhalli a jihar.
Kwamitin, karkashin jagorancin Shugaban ma’aikatan jihar, Liman Sani Kila, ya ce, dole ne mazauna jihar su daina aikata wadannan ayyukan domin kawo karshen ambaliyar ruwa ta dindindin.
- Babu Ranar Komawa Kananan Makarantu A Jihohin Kano Da Edo
- Yadda Ake Buga Wasannin Guje-guje Na Nakasassu A Paris
A kwanakin baya ne hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kaduna, KADSEMA ta bayyana cewa, fiye da gidaje 2000 ne ambaliyar ruwa ta shafa a kananan hukumomin Zariya da Sabon Gari da ke jihar kadai.
Dangane da haka ne Gwamna Uba Sani ya kafa kwamitin domin tantance irin barnar da ambaliyar ruwa ta yi a garin Muchia da karamar hukumar Sabon Gari da sauran wurare a jihar, tare da gano abubuwan da ke sanya yankunan ke fama da matsalar.
Shugaban ma’aikatan da ya jagoranci wasu ‘yan kwamitin a rangadin tantance wuraren da ambaliyar ruwa ta shafa a yankin, Sanatan Kaduna ta tsakiya, ya ce, Gwamna Uba Sani ya damu da halin da mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa ke ciki.
Sai dai, ya bayar da tabbacin cewa, Gwamnan ya kuduri aniyar daukar matakan da za su magance matsalar ambaliyar ruwa domin hana afkuwar wannan mummunan bala’i a nan gaba.
Talla