Ministan Kudi, kuma Ministan Tattalin Arziki, Wale Edun, a ranar Litinin, ya karyata rahotannin da ke cewa, an kara harajin kayayyaki da hada-hadar kudade (VAT) zuwa kashi 10 daga kashi 7.5 cikin 100.
Ministan, a cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu da kansa, ya tabbatar da cewa, harajin VAT kamar yadda yake kunshe a cikin dokokin haraji ta kasa, kan yadda ake amsa kan darajar kudaden cinikayya, yananan akan yadda aka san shi (7.5 cikin 100).
- Afrika Ta Kudu Na Neman Hadin Gwiwa Da Sin Wajen Zamanantar Da Kanta
- Babu Ranar Komawa Kananan Makarantu A Jihohin Kano Da Edo
“Har yanzu, harajin VAT yana nan a kashi 7.5 kuma wannan shine abin da gwamnati ke karba a kan hada-hadar kudade da ake biya musu haraji. Don haka, gwamnatin tarayya ko hukumominta ba za su yi wani abu da ya saba wa dokokin kasa ba.
“Tsarin gudanar da haraji a hukumance yana nan kan tsarika uku, wato manufofin haraji, dokokin haraji da sarrafa haraji. Dole ne duka ukun su haɗu da kyau don samun kyakkyawan tsarin kasafin kuɗi na gwamnati.
“Don tabbatarwa, harajin VAT yana nan akan kashi 7.5 kuma wannan shine abin da za a karba kan duk kayayyaki da hada-hadar da za a biya mata harajin VAT,” in ji Edun.