Hukumar tsaro ta farin kaya ta saki shugaban kungiyar kwadago ta Nijeriy (NLC), Joe Ajaero bayan kama da shi da ta yi a ranar Litinin.
Rahotanni sun ce duk da an saki Ajaero, hukumar ta DSS ta kwace masa fasfo dinsa.
- Shugaban Zimbabwe: Zimbabwe Da Sin Na Da Matsaya Daya A Gaban Kalubaloli
- Kasar Sin Za Ta Hada Hannu Da Kasashe Mambobin FOCAC Wajen Aiwatar Da Sakamakon Taron Dandalin Domin Alummomin Bangarorin Biyu Su Amfana
An kama Ajaero ne a filin tashin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja yayin da yake hanyarsa ta zuwa wani taron kungiyoyin kwadago a Birtaniya.
Rahotanni sun ce Ajaero ya tabbatar da sakin nasa, inda ya bayyana cewa hukumar ta DSS ta bar shi ya tafi gida da misalign karfe 11 na daren Litinin.
Shugaban kungiyar kwadagon, ya bayyana cewa an yi masa tambayoyi na tsawon sa’o’i 15 bayan an kama shi da misalin karfe 7 na safe.
Bayanai sun yi nuni da cewa jami’an DSS sun masa tambayoyi kan zanga-zangar tsadar rayuwa da aka yi a farkon watan Agusta.
Kama Ajaero na zuwa ne kasa da makonni biyu bayan da ‘yansanda suka gayyace ahi zuwa ofishinsu a Abuja kan zargin hannu a ayyukan ta’addanci.