Shugaban Jami’ar Tarayya ta Kashere, Farfesa Umar Pate, ya bayyana matuƙar damuwarsa kan yadda matasan Nijeriya ke salwantar da basira da lokacinsu wajen hakar ma’adanai don neman arziki cikin gaggawa.
Ya bayyana hakan ne a Gombe yayin wata tattaunawa da manema labarai a ranar Laraba 11 ga watan Satumban 2024, yayin taron kasa da kasa na ƙungiyar ƙwararrun masu nasiha da bayar da shawarwari a Nijeriya (APROCON) karo na 8.
- Gwamnan Zamfara Ya Kaddamar Da Rabon Naira Biliyan 11 Na Bunkasa Ilimin Mata A Jihar
- Ambaliyar Ruwan Maiduguri Ta Shafi Mutane Sama Da Miliyan 1 – Gwamnati
Farfesa Pate, ya koka kan cewa matasa da yawa suna sha’awar hakar ma’adinai tare da tsammanin yin arziki cikin ƙanƙanin lokaci, wanda babu tabbas, kuma daga ƙarshe ke haifar da mummunan sakamako garesu.
Kazalika ya ci gaba da bayyana cewa, matasan da ke samun maƙudan kuɗaɗe da wuri a rayuwarsu sukan faɗa munanan halaye masu cutarwa da ɓata tarbiyyar kamar caca da shaye-shayen miyagun kwayoyi da sauransu, wadanda hakan ke gurgunta ci gaban al’umma.
Ya nemi iyaye da su lura da tarbiyyar ‘ya’yansu tare da bayyana buƙatar samar da tsarin ilimi da za dauki kwararan matakai wajen magance matsalolin inda Ita ma gwamnati ya ja hankalinta na samar da tsare-tsare da za su sauya tunanin matasa game da batun yin arziki cikin gaggawa.