A yau ma shafin ADABI na dauke da tattaunawa da wata matashiyar marubuciya, SALMA AHMAD ISAH wadda ta bayyana wa masu karatu yadda ta sha gwagwarmaya wajen fara rubutu. Marubuciyar ta yi bayanai masu yawa game da rubutu har ma da wasu batutuwan masu yawa. Ga dai tattaunawar tare da FATIMA ZARAH MAZADU (PRINCESS FATIMA) kamar haka:
Da farko masu karatu za su so su ji cikakken sunanki…
Sunana Salma Ahmad Isah.
Ko za ki iya fada wa masu karatu dan takaitaccen tarihinki?
Eh to, da farko dai an haife ni a garin Hadejia, jihar Jigawa. Na yi ‘Primary school’, har zuwa ‘Senior Secondary School’ duka a cikin garin Hadejia, kuma har kawo yanzu ina rayuwa a cikin garin Hadejia.
Me ya ja hankalinki har ki ka tsunduma fannin rubuce-rubuce?
A zahirin gaskiya na gano cewa rubutu wata hanya ce wadda zan iya amfani da ita wurin busawa mafarkaina rai, sannan hanya mafi sauki wurin isar da sako zuwa ga al’umma. Wannan shi ne abin da ya ja hankalina a kan rubuce-rubuce.
Ya gwagwarmayar farawar ta kasance?
Tun ina makaranta nake sha’awar karance-karancen litattafan Hausa, irinsu Jiki Magayi, Komai Nisan Dare, Uwar Gulma da dai makamantansu. A gaskiya wannan shi ne abin da ya fara ba ni sha’awa, sannan na ji cewar ina son ni ma na fara rubutu. To daga haka ne na fara rubuta ‘yan gajerun labarai a bayan litattafaina na makaranta. Kuma tun a wancan lokacin idan na yi na kan ba wa malaminmu na Hausa a makaranta ya duba min. Ganin yadda yake yabawa da kwazon da nake a rubutun ya sa na kara jajircewa ina rubutu ina ajewa, a wasu lokutan kawayena ma kan karba domin su karanta. Tun ina rubuta labarin da bai fi layi biyar ba, har na zo ina cika littafi da rubutu. To daga wannan lokacin ne na daina rubutu a takarda, na fara rubutu a waya. Har Allah ya sa yayata Fatima Ahmad Isah, ta ba ni shawarar tun da na iya rubutun labari kuma ya ba da ma’ana haka, me zai hana na fara rubutu onlayin. To da wannan shawarar ta ta na tsunduma harkar rubutun onlayin, har kawo yau.
Ya farkon farawar ta kasance?
Lokacin da na fara rubutun onlayin na fara da shiga kungiyar marubuta ne, domin koyon ka’idojin rubutun Hausa da Adabi, kuma daga nan ne na fara tasawa har zuwa yau.
Ya batun iyaye lokacin da za ki fara rubutu shin kin fuskanci wani kalubale daga gare su ko kuwa?
A gaskiya na fuskanta, lokacin da ina rubutawa a cikin litattafaina na makaranta idan na zo na ce litattafina ya cika a saya min sabo sai iyaye na su ce ai idan an saya min ma bata shi nake da rubutun wofi. Ko a ce ba za a siya min ‘pen’ ba saboda zan karar da shi a wurin rubutun shirme. Amma daga baya da suka gane cewa rubutun baiwa ce wadda Allah ya azurtani da ita sai suka hakura, domin yanzu komai na yi a kan rubutu sai dai san barka da jinjina.
Kamar wane irin labari kika fi mayar da hankali a kai wajen rubutawa?
Labaran ban tausayi su ne labaran da nake maida hankali wurin rubutawa.
Ko wane tsawon lokaci ne kika kwashe kina rubuta zuwa yanzu?
A kalla yanzu ban wuce shekara daya da fara rubutu ba.
Daga lokacin da ki ka fara zuwa yanzu kin rubuta labarai sun kai kamar guda nawa?
Daga lokacin da na fara kawo yanzu na rubuta litattafai guda biyar (5).
Wane labari ne ya zamo bakandamiyarki cikin labaran da ki ka rubuta?
A kaf cikin litattafaina guda biyar na fi son HASKE.
Wane labari ne ya fi baki wahala wajen rubutawa kuma me ya sa?
JUYIN KWADO ya fi kowanne bani wahala a cikin litattafaina, dalili kuwa shi ne; labarin ya sha bamban da irin wanda aka saba gani. Labarin JUYIN KWADO labari ne da ya kunshi rayuwa a zamani guda biyu, 11th century da 21st century. Hakan ta sa ya ba ni wahala sosai wurin rubuta shi.
Shin kin taba buga littafi?
A gaskiya har zuwa yanzu ban taba buga littafi ko guda daya ba, ina sa ran buga litattafina na LABARINSU.
Kamar wane irin nasarori ki ka samu game da rubutu?
Alal hakika na samu nasarori da dama ta dalilin rubutu, domin ta dalilin wannan rubutun mutane da dama sun sanni, sannan na samu alkairai da dama. Bugu da kari mutane da dama kan min alfarma ta dalilin rubutun.
Ko akwai wani kalubale wanda ki ka taba fuskanta game da rubutu ko daga wajen su kansu marubutan ko kuma makaranta?
Game da rubutu kam babu, haka ma daga wurin makaranta ban taba samu ba, kuma ba na fatan samu ko a nan gaba.
Wane abu ne ya taba faruwa da ke na farin ciki ko akasin haka game da rubutu wanda ba za ki manta da shi ba?
Akwai wacce ta taba bata min rai game da rubuta, lokacin ina rubuta littafin LABARINSU, kasancewar labari ne a kan illar fyade, kuma fyaden ya afku a kan jarumar labarin, sai wata ta yi min magana kan sam ita ba ta so aka ce an yi wa wance fyade ba. Gaskiya lokacin na ji ba dadi, domin burina shi ne nusar da jama’a illar fyade, amma sai na ga kamar ita ba ta fahimci inda na dosa ba. Dangane da yabo kuwa wannan ba a magana, jama’a da dama na yabawa da rubutun da nake.
Wane abu ne idan ki ka tuna da shi ki ke jin dadi sanadiyyar rubutu?
Idan na tuna da yadda jama’a ke yabon labaran da nake rubutawa kan sa na ji dadi a raina.
Ya ki ka dauki rubutu a wajenki?
Na dauki rubutu a matsayin hanyar busawa mafarkaina rai, sannan hanya mafi sauki don isar da sako.
Mene ne burinki na gaba game da rubutu?
Burina shi ne fara ‘scriptwriting’, wannan shi ne babban burina da nake fatan Allah ya cika min shi.
Wace ce gwanarki cikin marubuta?
Khadeeja Candy ita ce gwanata a kodayaushe.
Bayan rubutu kina wata sana’ar ne?
Eh! bayan rubutu ina sana’ar dinki, sannan ina ‘graphic design’.
Ya ki ke iya hada rubutu da dinki da girafik din da ki ke yi?
Eh! to, ko wanne a cikinsu ina ware masa lokacin da zan yi shi, misali na kan ware safiya a matsayin lokacin da zan yi aikina na ‘graphic design’, ko dinki idan ya samu, dare kuma na ware shi a matsayin lokacin da zan yi rubutu.
Wane sako ki ke da shi zuwa ga masoyanki masu karanta labaranki?
Abin da zan ce ga makaranta labarina shi ne, a duk sanda na rubuta labari, bai kamata ku dauka cewa abin da kuke tunani shi ne zai faru ba, domin yadda nake tunani ya bambanta da yadda kuke. Dan haka idan ba zai zamto daya ba, kuma babban burina shi ne ku fuskanci darasin dake cikin labarin, ba wai son ranku ba.
Ko kina da wadanda za ki gaisar?
Ina gaida Khadeeja Candy, my role model, da Zahra Royal Star babbar kawata, tare da Maryam Tijjani Muhammad, da Fatima Ahmad Isah da kuma babbar kawata Maimuna Muhammad.