Majalisar Gudanarwar Jami’ar Bayero da ke Kano, ta amince da É—aga darajar Dr. Maryam Mansur Yola, ta Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, da ke Jami’ar zuwa matsayin Farfesar Magungunan Gargajiya da Al’adu, kamar yadda wata sanarwa da Jami’ar ta fitar a ranar Juma’a 27 ga Disamba, 2024 ta bayyana.
Farfesa Maryam Yola, ‘yar asalin Æ™aramar hukumar Kano Municipal, ita ce mace ta farko a tarihi da ta zama farfesa kan magungunan gargajiya da al’adun Hausa, kuma malama ce da ke koyar da kwasa-kwasan Al’adun Bahaushe da ta koyar da É—umbin É—alibai a matakan ilimin daban-daban a ciki da wajen Nijeriya.
- Ɗaliban Jami’ar Bayero ‘Yan Ajin 2015 Sun Zamanantar Da Ɗakin Karatu Na M.A.Z Sani
- Za Mu Sabonta Dakin Karatu Na Sashen Harsunan Nijeriya Na Jami’ar Bayero — Hassan Baita
Farfesa Yola, mace ce da ta yi fice kan bincike a fannin magungunan gargajiya tun daga digirinta na farko, inda ta yi akan darussan Hausa a shekarar 1990, ta yi digirinta na biyu kan al’adun Bahaushe a shekarar 1997. Farfesa Yola ta kuma kammala karatunta na digiri na uku a shekara ta 2017, duka a Jami’ar Bayero. Kazalika, Farfesar ta yi babbar difiloma kan harkokin koyar da ilmi (PDE) a Kwalejin Shari’a ta Malam Aminu Kano (Legal) da ke Kano, inda ta kammala a shekarar 2015, ta kuma samu Æ™arin wasu takardun shaidar ilimi a wasu kwasa-kwasai da dama.
Baya ga takardu da maÆ™alu masu tarin yawa da ta gabatar kan magungunan gargajiya a jami’o’i da makarantu da wuraren tarukan ilimi daban-daban a ciki da wajen Nijeriya, ta duba aikin É—alibai masu tarin yawa a matakin digiri na É—aya da na biyu da na uku a Jami’ar Bayero da wasu Jami’o’i a Nijeriya.
Farfesa Yola, ta kuma riÆ™e muÆ™amai da dama a matakin gwamnatin tarayya da jiha da wasu kungiyoyin siyasa da jami’a da Æ™ungiyoyin ci gaban al’umma.
Farfesa Mansur Yola, mamba ce a Ƙungiyar malaman Jami’o’i ta Æ™asa (ASUU), kazalika mamba ce a Ƙungiyar Mata ta (ASFECOM), da kuma hukumar da ke bayar da shaidar malanta ta Nijeriya (TRCN).
A zamanin mulkin Gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ta riƙe Shugabar Hukumar Ilimin bai-ɗaya ta Jihar Kano daga 2008 zuwa 2011, da sauran muƙaman gwamnati da siyasa da dama a matakai daban-daban.
Ana sa ran É—aga darajar Fafesar zuwa wannan mataki zai Æ™ara mata himma da Æ™warin gwuiwar ci gaba da bayar da gudunmowa wajen inganta harkokin magungunan gargajiya a Nijeriya, ta hanyar amfani da É—imbin ilimi da Æ™warewarta a fannin, tare da bunÆ™asa al’adun Hausa, da cike giÉ“in da ake da shi a É“angarorin magungunan gargajiya da al’adun Hausa.