Ana iya bayyana dabarun koyarwa wata hanya ce ta koyarwa wadda ta dogar kan shi Malamin wanda yake bayyana abin da bakinsa ga wadanda suke koyo, ba tare da basu damar su yi tambaya lokacin da ake koya masu.
Amma bayn ya gama yi masu bayani ko kuma bayan daukar maganar kan maudu’in da yayi bayani inda kuma yake Kallon maganar ta shi dabara ce ta koyar da ilimi.(Noor Center, 2011).
- Sin Ta Kulla Yarjejeniyar Tsarin Kafa Huldar Abota Ta Raya Tattalin Arziki Cikin Hadin Gwiwa Tsakaninta Da Kasashen Afirka 22.
- Me Ya Haddasa Cacar Baki Tsakanin Kwankwaso Da PDP?
Wannan dabarar ta tsaya ne kan Malami wanda shi ne wanda aka maida hankali kan shi,dabarar da yake amfani da ita ta hanyar kalmomi,wanda hakan yana nufin yana bada labari ne akan maudu’in, wanda zai ci gaba da hakan,ba tare da wata tsayawa ba fiye da minti 5.Game da ita laccar abin yana nuna shi Malami yana bada labari ne da kuma ilimi ga su masu koyo a cikin murya mai karfi, wannan dabarar ana kiranta ana kiranta dabarar bada labari.Wannan dabarar koyarwar tana bukatar Malamai ya kasance ya iya tsara yadda zai koyar da darasin da kuma yadda zai koyar da darasin wajen amfani da magana da kuma samar da hujjoji akan wasu abubuwan da basu yi kama da ita ba.Wato kamar amfani da fuska, kallo da idanu,sai kuma yadda lamarin zai tafi daidai da yadda maganar take, kai har ma da amfani da wadansu abubuwa da kuma misalai domin a jawo hankalin wadanda ake koya mawa wajen maida hankalinsu ga darasin.akwai karin hanyoyi da yawa inda ita dabarar koyarwar ta kan karu,wanda abin ya hada da shi mai koyo kamar wata korama ce wadda bata da ruwa sosai, domin shi Malami tamkar wani rumbu ne da ake ajiye ilimi,hakane ma ita hanayar koyarwa wata hanya ce da ake cike koramar da bata da ruwa asa mata ilimi.A nan shi mai ba wanda ya samar da ilimin bane koyo an kuma haife shi da ilimin bane, shi yasa lamarin koyarwa anan tamkar a shiryawa bayan koya wa shi mai koyon yadda zai tafiyar da rayuwarsa wajen samar masa da ilimi, labari, da kuma kwarewa da zata taimaka ma shi a rayuwarsa ta gaba, domin Malami shine babban wanda yake bada muhimmiyar gudunmawa ga yadda rayuwar shi mai koyon ko masu koyon zata kasance nan gaba, wato shi mai koyon da kuma laccar da Malamain yayi amfani da ita wajen isar da sakon sa (Aziz, Khaled, 2012).
Ga yadda ake bukatar muhimman matakan da suka dace ayi amfani da su yadda dabarar lacca ta kamata kasance, kamar haka (Aziz & Khaled, 2012; Noon Center, 2011):
1)Lacca:Lacca ita tana da amfani wajen manya domin tana kai ga saB ayi tattaunawa wanda kuma hakan ba zai shafi tambayoyin ba sai dai a karshen laccar.
2)Bayani: Bayani da kwatanta yadda su dalibai za su gane ko fahimta.Wannan ya hada da amfani da harshen da ake koyarwar cikin sauki wato daga mai sayki zuwa ga mai wahala,daga wanda aka sani zuwa wanda ba a sani ba, daga gaba daya zuwa wani bangare.
3)Yin bayani: Wannan it ace dabarar koyarwa da tafi muhimmanci inda za ayi magana da baki domin a samu fahimtar yadda lamarin yake.
4)Labaru:Wani nau’i ne na gabatar da darasi ta dabarar lacca wajen koyawa dalibai da niyyar jan hankalinsu ta hanyar amfani da sadarwa da abubuwan da aka yi ko aka sani domin suma su amfana.
5)Maimaita abinda Malami ke cewa:Anan Malami shine za iyi wasu abubuwa ko yadda za ayu su, su kuma masu koyo su rika yin yadda ya ambata, bayan ya ambata ko su yi abinda suka ga shima yayi.
Yana da kyau gareka kayi amfani bayan an kammala dabarar koyarwa ta lacca, da wasu hanyoyida za su auna fahimtar su masu saurare abinda suka koya daga abubuwan da aka yi amfani dasu, wajen wadansu tambayoyi ko tsari na a dawo baya, ba domin komai ba sai saboda a kara fadada shi maudu’in da Malamai yake magana akan shi,ta haka ne kuma su masu koyo su iya bada amsar, ko kuma su koma kan misalan da ya basu domin zame masu fitila idan sun shiga duhu.Ita dabarar koyar da laccar tana iya yin amfani a wasu wurare kamar lacca ta wayar da kan ‘yan kasa kan lamarin da ya shafi ilimin kula da lafiya, hana aukuwar hadari,wayar da kai dangane da lamarin addini da al’ada,da sauran darussa wadanda suke dauke da bayanai, abin har ya kai masu saurare da yawa (Ahmad, 2005).