• English
  • Business News
Wednesday, July 2, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Me Ya Haddasa Cacar Baki Tsakanin Kwankwaso Da PDP?

by Yusuf Shuaibu
10 months ago
in Tambarin Dimokuradiyya
0
Me Ya Haddasa Cacar Baki Tsakanin Kwankwaso Da PDP?
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Cacar baki ta kaure a tsakanin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP a zaben 2023, Rabiu Musa Kwankwaso da jam’iyyar PDP.

Zazzafar mahawarar dai ta fara ne tun lokacin da Kwankwaso ya bayyana cewa jam’iyyar PDP ta mutu a siyasance.

  • ‘Yan Bindiga Sun Sace Matafiya A Babbar Hanyar Gusau-Funtua
  • Kotu Ta Bada Belin Masu Zanga-Zangar Tsadar Rayuwa Kan Naira Milyan 10 Kowanensu

Da yake magana a ranar Asabar a yayin bude wani ofishin jam’iyyar NNPP da aka yi wa gyara a Jihar Katsina, Kwankwaso ya ce shi da mabiyansa sun bar PDP ne saboda ta mutu.

“Ina so in tunatar da ku cewa PDP ta mutu saboda mun bar jam’iyyar. Tun da sun fita daga layi sai muka yanke shawarar ficewa,” in ji shi.

Kwankwaso ya kuma ce shi ne zai lashe zaben shugaban kasa a 2027, inda ya ce jam’iyyar NNPP a shirye take ta karbi ragamar shugabancin kasar da sauran jihohi.

Labarai Masu Nasaba

Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin Fadar Shugaban Kasa Da Peter Obi Kan Tallafin Mai

Sauya Sheka Ya Sa APC Ta Samu Gagarumin Rinjaye A Majalisun Tarayya

Tsohon gwamnan Jihar Kano ya ce bai kamata a yaudari ‘yan Nijeriya da kyauta ko kudi ba a lokacin zabe mai zuwa.

Da take mayar da martini, jam’iyyar PDP ta bayyana cewa Kwankwaso bai da alkibla a siyasar Nijeriya, wanda hakan ta sa ya gaza ya kuma rasa kimansa.

Jam’iyyar PDP ta mayar da martanin ne a cikin wata sanarwa ta hannun sakataren yada labaranta na kasa, Debo Ologunagba, ta soki Kwankwaso da nuna son kai da son zuciya wanda ke nuni da cewa shi ba shugaba ne nagari ba.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Martanin da muka mayar dangane da kalaman da Sanata Rabi’u Kwankwaso shi ne, ba shi da wani tasiri a siyasar Nijeriya a yau idan aka yi la’akari da yadda yake fafutukar shugabancin jam’iyyar mai suna NNPP wadda ita ma ke fafutukar ganin ta mallaki jiha daya kawai.

“Abun takaicin ne a cewa dan siyasar da ya gaza kuma mara tasiri da ke da jiha daya zai yi ikirarin cewa jam’iyyar da ke da gwamnoni 13, da sanatoci da dama da ‘yan majalisar wakilai masu yawa da a dukkan rassan kasar nan.

“Abin da ya fi tayar da hankali shi ne, yadda Sanata Kwankwaso ya nuna tsananin son kai da son zuciya, wanda hakan ke nuna cewa shi ba shugaba ba ne.”

Jam’iyyar PDP ta bayyana Kwankwaso a matsayin dan siyasar mara alkibla da wanda ya samu nasarorinsa ta hanyar tsarin jam’iyyar PDP.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Abin takaici ne a wannan lokaci da jam’iyyar PDP da ‘yan Nijeriya masu kishin kasa ke tofa albarkacin bakinsu dangane da tsananin wahalhalun da kasar nan ke fuskanta sakamakon manufofin gwamnatin APC na kin jinin jama’a, a wannan lokacin ‘yan Nijeriya ciki har da gidan Sanata Kwankwaso na Jihar Kano na fama da yunwa.

“A daidai lokacin da ‘yan Nijeriya sama da miliyan 150 suka tsunduma cikin bakin talauci, a kullum miliyoyin ‘yan Nijeriya ke asarar hanyoyin samun abinci a lokacin da darajar naira ta fadi zuwa fiye da naira 1,600 kan dala daya, sannan an samu kashi 34 na hauhawar farashin man fetur wanda ya kai lita daya naira 1,200 a sannan kasar nan sakamakon munannan manufofin APC. Burin Sanata Kwankwaso shi ne son zama shugaban kasa ba tare da nuna damuwa kan halin da kasar nan ke ciki ba. Wannan babban abin takaici ne matuka.

“Don haka jam’iyyar PDP ba za ta tsaya cacar baki da shi ba kan irin wannan nuna son kai da rashin sanin ya kamata. Ko ta wace fuska, duk nasarar da Kwankwaso ya samu a siyasance, ya samu ne ta sanadiyyar PDP.”

Wannan dambarwa dai ta sake jefa shakku a kan yiwuwar kawancen da ake tunanin zai iya kulluwa a tsakanin Atiku da Kwankwaso da kuma Obi domin yi wa Shugaban Kasa Tinubu taron dangi a shekarar 2027.

Kana tambayar da ake dakon amsarta har yanzu ita ce, me ya haddasa wannan cacar bakin a tsakanin Kwankwaso da PDP?


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: kanoKwankwasoPDPSiyasa
ShareTweetSendShare
Previous Post

Muna Fatan Sterling Ya Bai Wa Mara Ɗa Kunya A Arsenal – Arteta

Next Post

Sin Na Shirin Soke Daukacin Haraji Kan Hajojin Dake Shiga Kasar Daga Kasashe Mafiya Karancin Wadata

Related

Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin Fadar Shugaban Kasa Da Peter Obi Kan Tallafin Mai
Tambarin Dimokuradiyya

Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin Fadar Shugaban Kasa Da Peter Obi Kan Tallafin Mai

3 weeks ago
APC
Tambarin Dimokuradiyya

Sauya Sheka Ya Sa APC Ta Samu Gagarumin Rinjaye A Majalisun Tarayya

3 weeks ago
Adawa
Tambarin Dimokuradiyya

Yadda Rarrabuwar Kawunan Jam’iyyu Zai Iya Sauya Alkiblar Zaben 2027

4 weeks ago
‘Yancin Kananan Hukumomi: Shekara Daya Da Hukuncin Kotun Koli Amma Ba A Aiwatar Ba
Tambarin Dimokuradiyya

‘Yancin Kananan Hukumomi: Shekara Daya Da Hukuncin Kotun Koli Amma Ba A Aiwatar Ba

1 month ago
Ko Kwamitin Saraki Zai Iya Ceto PDP Daga Rikicin Cikin Gida?
Tambarin Dimokuradiyya

Ko Kwamitin Saraki Zai Iya Ceto PDP Daga Rikicin Cikin Gida?

1 month ago
Tsadar Rayuwa Da Karuwar Ta’addanci Na Ci Gaba Da Tagayyara ‘Yan Nijeriya
Tambarin Dimokuradiyya

‘Yan Adawa Na Cacakar APC A Yankin Arewa Maso Yamma Bisa Goyon Bayan Tazarcen Tinubu

1 month ago
Next Post
Sin Na Shirin Soke Daukacin Haraji Kan Hajojin Dake Shiga Kasar Daga Kasashe Mafiya Karancin Wadata

Sin Na Shirin Soke Daukacin Haraji Kan Hajojin Dake Shiga Kasar Daga Kasashe Mafiya Karancin Wadata

LABARAI MASU NASABA

An Dakatar Da Shugaban APC Na Jihar Nasarawa

An Dakatar Da Shugaban APC Na Jihar Nasarawa

July 1, 2025
Tawagar Gwamnatin Tarayya Da Ɗangote Sun Halarci Jana’izar Aminu Ɗantata A Saudiyya

Tawagar Gwamnatin Tarayya Da Ɗangote Sun Halarci Jana’izar Aminu Ɗantata A Saudiyya

July 1, 2025
An Gudanar Da Bikin Daga Tuta Da Bikin Murnar Cika Shekaru 28 Da Dawowar Yankin HK Karkashin Kasar Sin

An Gudanar Da Bikin Daga Tuta Da Bikin Murnar Cika Shekaru 28 Da Dawowar Yankin HK Karkashin Kasar Sin

July 1, 2025
Ɗantata: Majalisar Dattawa Ta Ɗage Taron Jin Ra’ayin Jama’a A Arewa maso Yamma

Ɗantata: Majalisar Dattawa Ta Ɗage Taron Jin Ra’ayin Jama’a A Arewa maso Yamma

July 1, 2025
Kayan Aro Baya Rufe Katara

Kayan Aro Baya Rufe Katara

July 1, 2025
Gwamnatin Zamfara Ta Tabbatar Da Kashe Manyan Mayakan Bello Turji Fiye Da 100

Askarawan Zamfara Sun Kashe Riƙaƙƙen Ɗan Bindiga, Kacalla Ɗanbokolo Ubangidan Turji

July 1, 2025
Tawagar Likitoci Ta Sin Ta Ba Da Horon Fasahar Likitancin Gargajiya Ta Sin A Nijar

Tawagar Likitoci Ta Sin Ta Ba Da Horon Fasahar Likitancin Gargajiya Ta Sin A Nijar

July 1, 2025
Farfesa Haruna Musa Ya Lashe Zaɓen Shugabancin Jami’ar Bayero Ta Kano

Farfesa Haruna Musa Ya Lashe Zaɓen Shugabancin Jami’ar Bayero Ta Kano

July 1, 2025
Fahimtar Sabon Tunani: Yadda Sin Ta Samu Bunkasa A Tarihi Ta Hanyar Juyin Juya Halin Da Take Yi Wa Kanta 

Fahimtar Sabon Tunani: Yadda Sin Ta Samu Bunkasa A Tarihi Ta Hanyar Juyin Juya Halin Da Take Yi Wa Kanta 

July 1, 2025
An Yi Bikin Kade-Kade Don Taya Murnar Cika Shekaru 104 Da Kafuwar JKS

An Yi Bikin Kade-Kade Don Taya Murnar Cika Shekaru 104 Da Kafuwar JKS

July 1, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.