A wani muhimmin mataki na wanzar da zaman lafiya da hada kan matasa, an kammala gasar lashe kofin ‘Unity cup’ na Gwamna Uba Sani wanda Akanta Janar (AG), Bashir Suleiman Zuntu ya shirya wa matasan Kubau kuma ya ɗauki nauyi.
Gasar ta kwallon kafa, ta kwashe kimanin Mako 6 ana gwabzawa a tsakanin kungiyoyi 32 da suka fito daga sassa daban-daban na yankin mazabar Kubau, da ke shiyya ta daya a Kaduna.
- Gwamna Uba Sani Zai Kaddamar Da Kwalejin Koyon Aikin Jinya Da Ungozoma A Pambegua
- Kaduna: Ruftawar Hanya Sakamakon Ambaliyar Ruwa Ta Katse Garuruwa Biyar A Lere
An kamala gasar ne a ranar Lahadi, 15 ga watan Satumba, 2024 a filin wasa na Zuntu Township.
AG Bashir, ya bayyana jin dadinsa da yadda yaga al’ummar yankin sun taru wuri guda suna nishadi ba tare da nuna banbancin yare ko wata wariya ba, inda ya kara da cewa, wannan shiri za a inganta shi, kuma zai ci gaba da gudana.
Da yake bayyana muhimmancin gudanar da wasanni a tsakanin Matasa, musamman wasan kwallon kafa, AG ya ce, “kwallo tana da farin jini a tsakanin matasan yankin, inda ta sake hada kawunansu, kowa ke jin dadin zama da juna ba kyara ba tsangwama.”
Ya kuma bayyana jin dadinsa da yadda matasan ke bin tsarin doka, babu hatsaniya, kowa na tsayawa inda jami’an tsaro suka umurta da a kiyaye.
Ya kuma yi kira ga matasa da cewa, akwai hanyoyin samun nasara a rayuwa da yawa, musamman a bangaren wasanni, ba dole ba ne, sai mutum ya yi aikin Gwamnati, ko Kasuwanci, ko Siyasa, ne zai yi nasara ba. Inda ya buga misali da cewa, “Ga Shahararren dan wasan kwallon kafa kuma kaftin din tawagar kwallon kafa ta Nijeriya da yake tare da mu a wannan filin wasa, Ahmed Musa, ya zama mutum mai nasara a rayuwa ta hanyar wasan kwallon kafar, kuma kowa ya son shi da taimakon matasa sanadiyyar wannan Nasarar”.
Ahmed Musa, akan abinda ya saba na taimakon matasa don ganin sun cimma burikan su na samun nasara, ya yi alkawarin fitar da ‘yan wasa 6 da suka yi fice a gasar zuwa kasashen ketare.
AG Bashir, Ya kuma nanata alkawarin Gwamna Uba Sani cewa, nan ba da jimawa ba, za a fara aikin gyaran filin wasa na Sir Ahmadu bello da ke Kaduna (ASB), kuma kungiyar kwallon kafa ta Kaduna United, da tuni ta fita acikin jerin kungiyoyin da suke buga gasar Firimiya ta Nijeriya, za ta komo cikin jerin kungiyoyin.
Ya kuma gode wa Gwamna Uba Sani, kan kudirinsa na maido da Kaduna United cikin jerin kungiyoyin Firimiya.
Daga cikin fitattun ‘yan wasan kwallon kafa da suka halarci wasan karshen, akwai Ahmad Musa da Shehu Abdullahi duka, su biyun, suna daga cikin tawagar kwallon kafa ta Nijeriya (Super Eagles).
Tun da Farko, Hon. Musa Danjuma Bello, Shugaban Shirya gasar kofin ‘Unity Cup’, ya bayyana cewa, an shirya gasar ne domin wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin matasan Karamar hukumar Kubau.
“Wannan gasar, ta tattaro kungiyoyin kwallon kafa 32, kuma kowacce kungiya za ta samu kyautar sunkin jesi da sauran kayayyakin kwallo. Bugu da kari, Kungiyar D.Officer FC wacce ta zama zakara, ta samu Karin kyautar kudi har Naira 500,000; Bagadaza FC wacce ta zama ta biyu, ta samu karin kyautar kudi naira 300,000 yayin da kungiyar Bugau FC ta samu karin kyautar kudi naira 200,000.
A nasa Jawabin, Kakakin majalisar jihar kaduna, Hon. Yusuf Liman ya nuna jin dadinsa da yadda yaga matasan Kubau, masoya kwallo a filin wasa na Zuntu township sun taru suna murnar wannan gasa, “lallai ya tabbata kwallo tana hada kan matasa”.
Liman, ya kuma jinjina wa kwamitin shirya wannan gasar lashe kofin hada kan al’umma ‘Unity Cup’ na Sanata Uba Sani wanda Akanta-janar, Hon. Bashir Suleiman Zuntu ya dauki nauyi.
Haka kuma, Dan Majalisa mai wakiltar mazabar Kubau, Shehu Yunus Pambegua ya nuna farin cikinsa da Allah ya kawo wannan rana da aka buga wasa na karshe na ‘Unity Cup’ kuma aka tashi lafiya.