Darakta janar na hukumar kula da hakkin mallakar fasaha ta duniya (WIPO) Daren Tang, ya yabawa kasar Sin bisa gagarumar gudunmuwar da ta bayar ga muhallin tabbatar da hakkin mallakar fasaha a duniya.
A zantawarsa da wata kafar yada labarai ta kasar Sin a birnin Beijing, Daren Tang ya bayyana irin ci gaba mai sauri da Sin ta samu wajen neman shaidar mallakar fasaha, inda kasar ta kasance kan gaba a duniya wajen neman wannan shaida.
- Kofin Gwamna Uba Sani: Ahmed Musa Ya Yi Alƙawarin Fitar Da ‘Yan Wasa 6
- Tawagar Majalisar Ɗinkin Duniya Ta Zayarci Maiduguri, Ta Yi Alƙawarin Ƙarin Tallafi
A cewar wani kwarya-kwaryan rahoto na hukumar WIPO kan alkaluman kirkire-kirkire a duniya na shekarar 2024, kasar Sin mazauni ne ga rukunonin kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha 26 daga cikin 100 dake kan gaba a duniya, inda ta ci gaba da rike kambunta a matsayin jagora a duniya a wannan fanni, tsawon shekaru 2 a jere.
A cewarsa, kokarin kasar Sin na neman ci gaba mai inganci zai kara karfafa bangarorin kimiyya da fasaha da kuma kirkire-kirkire. (Fa’iza Mustapha)