Hukumar kula da yanayin samaniya ta Nijeriya, NiMet, ta yi hasashen yanayi na tsawa da ruwan sama daga ranar Talata zuwa Alhamis a fadin kasar.
An fitar da hasashen ne a ranar Litinin a Abuja, inda hasashen ya nuna yanayin tsawa a sassan jihohin Bauchi, Kebbi, Taraba, Kano, Katsina, Adamawa, da Kaduna a safiyar ranar Talata.
- Kasar Sin Na Girmama Cikakken ‘Yancin Serbia
- Ambaliya: Atiku Ya Bai Wa Jihar Borno Gudummawar Miliyan 100
A cewar hukumar, ana sa ran za a yi tsawa a duk fadin yankin a cikin wannan ranar.
“A yankin Arewa ta tsakiya, ana sa ran tsawa a sassan jihohin Kogi, Benuwe, Filato, Babban Birnin Tarayya Abuja, Nasarawa da Neja da safe.”
Hukumar ta yi hasashen tsawa a sassan jihohin Taraba, Adamawa, Sokoto, Kebbi, Zamfara, Katsina, Kano da Kaduna a safiyar Laraba.
A cewar NiMet, ana sa ran za a yi tsawa a sassan jihohin Borno, Gombe, Adamawa, Taraba, Kano, Katsina da Kebbi da yammacin ranar.
“A yankin Arewa ta tsakiya, ana iya samun tsawa a sassan babban birnin tarayya, Kogi, Neja da Kwara da safe.”
Talla