Gwamnatin Zimbabwe ta amince da yanka giwaye 200 don ciyar da ‘yan kasar da ke fama da yunwa.
Mai magana da yawun hukumar kula da wuraren bude ido da shakatawa da namun daji na Zimbabwe, Tinashe Farawo, ya tabbatar wa kamfanin CNN shirin gwamnatin a ranar Litinin.
- Kwamitin Tallafin Karatu Na Sanata Maidoki Ya Tantance Dalibai Sama Da 805 A Kebbi
- An Masa Daurin Watanni 4 Kan Satar iPhone Guda 2
“Muna shirin yanka giwaye 200,” in ji Farawo, yayin da ya koka da yadda ake samun karuwar asarar rayukan dan Adam da giwayen ke murkushewa sakamakon tsananin fari a kasar da ya addabi yankin gabashin Afirka.
Ya kara da cewa: “Dabbobin suna yin barna sosai a cikin al’umma, suna kashe mutane. A makon da ya gabata mun rasa wata mata a yankin arewacin kasar da giwa ta kashe. A makon da ya gabata ma haka ta faru. Don haka, rage adadin giwayen, wata hanya ce ta magance asarar rayukan dan Adam”.
A cewar kafafen yada labarai na cikin gida, a bana, fiye da mutane 30 ne suka rasa rayukansu sakamakon harin namun daji a Zimbabwe.