Kwamitin bayar da tallafin karatu na Sanata Garba Musa Maidoki mai wakiltar mazabar Kebbi ta Kudu, ya biya wa jimillar dalibai sama da 805 domin samun tallafin karatu.
Biyan kudaden ya hada da dalibai 291 daga Jami’ar Aikin Gona ta Tarayya da ke Zuru (FUAZ) da kuma dalibai 514 daga Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kebbi da ke Aliero (KSUSTA).
- ‘Yan Bindiga Sun Kone Ofishin ‘Yansanda A AnambraÂ
- Yaƙi Da ‘Yan Bindiga: Yadda Gwamna Dauda Ya Karɓi Baƙuncin Babban Hafsan Tsaro
Sai dai kwamitin ya gano wani dalibi da bayanan da ya bayar ba su inganta ba, wanda hakan ya sa aka sallame shi daga tantancewar.
Bisa hakan ne kwamitin Suka sallami wanda aka gano daga rashin ba su kudin tallafin karatun.
Domin ka’idar shi ne sai wanda ya nuna shaidar zama dan kananan hukumomin da suka kunshin mazubun Kebbi ta kudu, ko daga masarautar Yauri ko Zuru.
Daliban da kwamitin ya tantance sahihincin takardun su sun karbi Naira 35,000 kowane bayan an kammala tantance su.
Shugaban kwamitin, Farfesa Umar Ahmad Sanda, ya bayyana jin dadinsa da aikin, inda ya yaba wa ‘yan kwamitin bisa kwazon da suka yi.
Farfesa ya bayyana cewa takardun da ake bukata sun hada da takardar zama dan asalin karamar hukuma, katin shaidar zama dan kasa, ba da izinin shiga jami’a, da katin shaidar zama ɗalibi a jami’a.
Dalibin da aka hana ya yi ikirarin cewa daga karamar hukumar Yauri ya fito amma takardun da aka gabatar sun nuna cewa mallakar karamar hukumar Birnin Kebbi ce.
Shugaban kwamitin ya bukaci dalibai da su yi watsi da kansu idan ba su da takardun da ake bukata, yana mai gargadin cewa bincike zai gano duk wanda bai da bayanan da suka dace.
Ya kuma yaba da goyon bayan da ‘yan kwamitin, shugabannin jami’a, da kuma Sanata Maidoki suka samu a bisa jajircewarsa na karfafa wa matasa musamman masu karatu a jami’o’in kasar nan.