Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Ganduje, ya karyata rade-radin da ake yadawa, cewa yana cikin wani shiri na tsige Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano.
Ganduje ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da babban mai taimaka masa na musamman kan wayar da kan jama’a, Cif Oliver Okpala ya fitar.
- Gwamnan Kano Ya Rushe Kantomomin Kananan Hukumomin Jihar Kano 44
- Kotu Ta Sanya Rana Kan Batun Tsige Ganduje A Matsayin Shugaban APC
Shugaban jam’iyyar APC na kasa yana mayar da martani ne kan wani rahoto da ke yawo a kafafen sada zumunta mai taken “Ganduje ya jagoranci wani sabon shiri domin tsige Sarki Mohammad Sanusi”, wanda ya yi zargin cewa “sabon makirci ne” da Ganduje ya shirya na tsige Muhammadu Sanusi daga mukamin Sarkin Kano.
Rahoton ya nakalto cewa, “Wasu majiyoyi daga fadar Kofar Kudu, sun ce, wasu masu fada a ji a Kano, a karkashin jagorancin shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje na kitsa yunkurin tsige tsohon gwamnan babban bankin Niojeriya (CBN) daga mukaminsa na Sarkin Kano”
Amma da yake mayar da martani ga rahoton, Ganduje ya ce, babu gaskiya a cikin ikirarin, yana mai cewa, ba shi da alaka da zargin wani sabon yunkurin tsige Sarki Sanusi na biyu.
Ganduje ya nanata cewa, ba shi ne gwamnan jihar ba, kuma ba shi ne shugaban majalisar dokokin jihar ba, don haka, ba shi da wani hurumi na nadi ko tsige wani a matsayin Sarkin Kano.