Tun bayan kammala taron koli na dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka na FOCAC a kwanan baya, masu fashin baki ke ta yin tsokaci game da tasirin dake tattare da dorewar hadin gwiwar Sin da kasashen nahiyar Afirka.
Da ma dai cikin sama da shekaru 70 da suka gabata, sassan biyu sun wanzar da dangantaka da abota da hadin kai a fannoni daban daban, wanda hakan ya haifar da sakamako mai gamsarwa. Kaza lika a shekarun baya bayan nan an ga yadda hakan ya ingiza hadin gwiwar cinikayya tsakanin Sin da Afirka zuwa matsayin koli, ta yadda ake hasashen dukkanin ci gaban da kasar Sin ta samu na iya yin tasiri mai kyau ga ci gaban kasashen Afirka baki daya.
- Sin Ta Harba Tagwayen Taurarin Dan Adam Na Tsarin BeiDou
- Yawan Mutanen Da Suka Shiga Da Fita Daga Kasar Sin A Hutun Bikin Tsakiyar Kaka Ya Zarce Miliyan 5.25
Yanzu haka dai kasar Sin ce kan gaba wajen yawan jari da sassan waje ke zubawa a kasashen Afirka, kana ita ce babbar abokiyar huldar cinikayya ta kasashen Afirka cikin shekaru 15 a jere. Wata kididdiga ma ta nuna yadda tsakanin shekarar 2000 zuwa 2023, adadin darajar cinikayya tsakanin Sin da kasashen Afirka ta karu daga kimamin yuan biliyan 100 zuwa tiriliyan 1.98, wanda hakan ke nuna karuwar kimamin kaso 17.2 bisa dari a duk shekara.
Wannan a fannin cinikayya da zuba jari ke nan. Wani fannin kuma mai matukar muhimmanci shi ne na bunkasa hada-hadar harkokin tattalin arziki da kudade, wanda suka kunshi samar da lamuni mai saukin ruwa, da tallafin jin kai, da gudanar da ayyukan samar da ababen more rayuwa bisa hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, wanda ko shakka babu ya sanya kasar Sin samun karin karbuwa tsakanin kasashen Afirka.
Bugu da kari, kasar Sin na mu’amala da kasashen Afirka bisa kare ’yancinsu na zabar hanyar neman bunkasuwa mafi dacewa da su, tare da cimma nasara bisa burikansu. Ya zuwa wannan lokaci, kamfanonin Sin sun gina tare da gyara sama da layin dogo da tsayinsa ya kai sama da kilomita 10,000, da hanyoyin mota masu tsayin kusan kilomita 100,000, da gadoji kusan 1,000, da kusan tashohin ruwa 100, baya ga turakun lantarki masu tsayin kusan kilomita 66,000, da manyan turakun sadarwa da tsayinsu ya kai kilomita 150,000 a sassan kasashen Afirka daban daban.
Masharhanta na ganin irin wadannan manyan ayyukan raya kasa dake gudana karkashin manufofin samar da ci gaba na Sin irin su shawarar “ziri daya da hanya daya” ko BRI, muhimman ginshikai ne dake kara dunkule nahiyar Afirka waje guda, da fadada hadewarta da sauran sassan duniya, ta yadda al’ummun Sin da na nahiyar Afirka za su cimma nasarar zamanantar da kansu, da kuma kaiwa ga gina al’ummar bai daya ta Sin da Afirka mai kyakkyawar makoma guda. (Saminu Alhassan)