Hukumar kula da harkokin shige da fice ta kasar Sin ta bayyana a yau Laraba 18 ga wata cewa, a hutun bikin tsakiyar kaka wato bikin Zhongqiu na shekarar da muke ciki, sassan kula da harkokin shige da fice a duk fadin kasar, sun ba da tabbaci ga mutane sama da miliyan 5.25 wadanda suka shigo da fita daga kasar yadda ya kamata, wato mutane miliyan 1.752 a kowace rana, adadin da ya karu da kaso 18.6 bisa dari, idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara.
Rahotanni sun ruwaito cewa, adadin mutanen dake zaune a babban yankin kasar Sin, da suka shiga da fita daga cikin kasar, ya karu da kaso 15.1 bisa dari, yayin da karuwar jamaar yankunan Hong Kong da Macau da Taiwan da suka shiga da fita daga cikin kasar ta kai kaso 7.3 bisa dari. Kana, yawan baki yan kasashen waje da suka shiga da fita daga cikin kasar Sin, ya karu da kaso 62.2 bisa dari. Har wa yau, adadin ababen hawa masu jigilar fasinjojin da suka shiga da fita daga kasar Sin da aka bincika, ya kai dubu 242, adadin da ya karu da kaso 37.6 bisa dari, idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara.
A yayin hutun bikin tsakiyar kaka na bana, hukumomin kula da harkokin shige da fice a duk fadin kasar Sin sun gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, inda kasa da mintuna 30, yan kasar Sin suke iya wucewa layi. (Murtala Zhang)