Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar ‘yan ta’adda ta ISWAP ce ta kai hari a wani shingen sojoji da ke unguwar Madalla a karamar hukumar Suleja a jihar Neja.
A ranar Juma’ar da ta gabata ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari kan sojojin masu gadi a kusa da dutsen Zuma da ke kan hanyar Abuja.
Muhammad Abdullahi, mai magana da yawun shugaban karamar hukumar Suleja, ya ce ‘yan bindigar sun kai hari da yawa a yankin.
Abdullahi ya kara da cewa abokin nasa da ke kusa da yankin a yayin harin ya ce maharan sun kashe jami’an soji biyu.
A cewar rahoton wata kungiya mai zaman kanta ta Amurka da ke bin kungiyoyin masu jihadi, ISWAP ta matso kusa da babban birnin Nijeriya tare da kai hari kan shingen sojoji.
Wannan shi ne hari na biyu da aka dangantawa da kungiyar a wannan watan.
A farkon watan Yuli, ISWAP ta dauki alhakin harin da aka kai gidan yarin Kuje da ke babban birnin tarayya, Abuja.
‘Yan bindigar sun kai hari a gidan gyaran halin, inda aka ce daruruwan fursunoni – da ke ciki har da wadanda ake zargin ‘yan Boko Haram ne – sun tsere.
Wani faifan bidiyo da aka ce hukumar A’maq ta wallafa, mujallar farfaganda da kungiyar ke amfani da ita, ta nuna yadda ‘yan ta’addan suka kai hari gidan yarin.
Kungiyar ISWAP da ta balle daga bangaren Abubakar Shekau na kungiyar Boko Haram, ita ce ta kai mafi yawan hare-hare a yankin arewa maso gabas.