Shafin taskira shafi ne da ya saba zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma.
Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da yanayi da halin da muke tsintar kammu a ciki duk shekara na samun ambaliyar ruwa a wasu garuruwa a Nijeriya.
- CBN Ya Kaddamar Da Sabbin Ka’idoji Ga Masu Harkar POS
- Xi Ya Jaddada Ba Da Cikakkiyar Dama Ga Fa’idar Siyasa Ta CPPCC
Kamar yadda wakiliyarmu BILKISU TIJJANI KASSIM ta tattaro mana, akwai wasu mutane da ke ganin hanyar da za a bi wajen magance yawan ambaliyar ruwa a wasu garuruwa a Nijeriya sun hada da rashin daukar matakan da ya dace tun farko daga gwamnati, musamman wajen fitar da hanyoyi da tituna da suka shafi hanyoyin ruwa musamman lokacin damina domin kiyayen hakkokin jama’a, wanda wannan ba karamin tasiri bane ga jama’a.
Rabi’atu Abdullah Muhammad
Assalamu alaikum Warahmatullah
Hanyoyi da ya kamata a bi wajen magance ambaliyar ruwa su ne, duk inda aka san hanyar ruwa ce kada a toshe ta, sannan kuma sai fadama wajen mazaunar ruwa nan ma kada a rufe shi idan ya zama dole sai an rufe to kada a rufe gaba daya sai a bar masa hanya ko kuma wajen fadamar a bar wani bangare kada a rufe gaba daya domin rufewa gaba dayan shike sa idan ruwa ya zo bai samu waje ko hanya sai ya shiga mutane. Allah ya sa mu dace, Allah ya bamu damuna mai albarka ya bamu wucewa lafiya.
Abdurrahman Tijjani
Assalamu alaikum
Hanyoyi da ya kamata a bi wajen magance Ambaliyar Ruwa a Nijeriya su ne, gwamnati ta tashi da gaske ta yi aiki domin fa sai an yi aiki na gaskiya shi ne duk inda aka san garuruwan da ruwa ya fiya yawan zuwa to ya kamata a yi musu hanyoyin ruwa manya-manyan kwalbati wanda idan ruwa ya zo zai iya wucewa ba tare da ya yi barnaba. Sannan kuma rufe hanyoyin ruwa da rufe fadamu su ne manyan abunuwan da yake kawo wannan Ambaliyar saboda da zarar ruwa ya zo hanyarsa ya ga babu inda zai wuce zai yi cikin gari ne, haka ma rufe fadama itama tana daya daga cikin babban abin da yake kawo Ambaliyar ruwa saboda idan ruwa ya zo wajensa ya tad da an rufe to fa zai yi kokarin zama a wajensa ne an ce shi ruwa ba ya manta wajensa ko ba jima ko ba dade sai ya dawo wajansa, to saboda haka rufe fadama gaskiya shima babbar barazana ce ga Ambaliyar ruwa a inda yake. Allah ya sa mudace
Ibrahim Musa Bala
Yadda gwamnati za ta bollowa ambaliyar da ta faru a garuruwa da dama a Nijeriya.
Ya kamata gwamnati ta gina hanyar wucewar ruwa yadda ruwan zai wuce ba tare da hawa kan hanya ba, sannan ta yi kokari karin ajiye abin zubar da shara saboda a daina zubawa ta ko ina don shi ma yana toshe hanyar wucewar ruwa. Sannan mutane ya kamata su bar gina gida a fadama don ruwa ba ya manta hanyarsa dole komai tsawon shekarun da ya dauka ba ya manta hanyar wucewarsa. Kuma Allah ya kara tsare mu baki daya kuma Allah ya kawo wa wadanda abin ya shafe su sauki
Alkazim Garba
Hanyar da gwamnati za ta iya bollowa da magance yawan Ambaliyar ruwa dake faruwa a garuruwa a Nijeriya su ne, da farko hanyar wucewar ruwa ya kamata ya zama a wadacce saboda wani lokacin idan an yi hanyar wucewar ruwa baya da zurfi shi ne idan an yi ruwan sama sai ya yi saurin hawa kan hanyar wuce wa hakan kuma sai ya haifar da ambaliya saboda haka a yi gini mai zurfi. Sannan gurin zubar da bola ya zama akwai tsafta saboda shi ma ya kan jawo ambaliya yayin da bola ta sauka kan hanya ta kan toshe hanyar wucewar ruwa.