Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal a ranar Lahadi ya ziyarci tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, don tattauna wasu batutuwa da suka shafi tsaron kasa.
Ganawar wadda aka gudanar a dakin karatu na Olusegun Obasanjo na Penthouse
- ‘Yan Kannywood Mu Guji Isar Da Sakon Da Bai Dace Ba -Yunusa Gaya
- Rundunar Sojin Saman Kasar Sin Ta Lashi Takobin Kare Cikakken ‘Yanci Da Yankunan Kasar
A wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Kehinde Akinyemi ya fitar, Tambuwal ya isa wurin da misalin karfe 1:30 na rana tare da wasu manyan mukarrabansa, inda kai tsaye ya shiga ganawar da tsohon shugaban kasar.
Sun fito ne da misalin karfe 2:40 na rana, kuma a takaice ana kyautata zaton taron ya shafi al’amuran kasa.
Daga bisani sun ci abinci shi da tawagarsa sannam suka nufi masallacin da ke cikin dakin karatun domin gudanar da sallah, kafin barin harabar.