Rahotonnin da ke fito wa daga Garin Yauri, a bayyana cewa wata dorinar ta yi kukan kura ta kai wa Mai -Gadin lambun Sarkin Yauri Dakta Muhammad Zayyanu Abdullahi a yayin da yake duba kifi a cikin kwale-kwale.
Abinka da tsautsayi, yana cikin kewaryar a wani rafi na cikin lambun sai ya iso daidai inda da wata Dorina take, ko da sukai arba sai ta fito daga cikin ruwa gurbinta ta afka masa inda ta samu nasarar taushe shi cikin ruwan kogi har ta kashe shi.
- Gwamnan Kebbi Ya Rantsar Da Zaɓaɓɓun Shugabannin Ƙananan Hukumomi
- Kwamitin Tallafin Karatu Na Sanata Maidoki Ya Tantance Dalibai Sama Da 805 A Kebbi
Majiyarmu ta Æ™ara da cewa”Dorinar ta haihu ne bisa ga haka, ta É—auki cewa za a É—auki É—iyar ta ne, sanadiyar hakan ta husata inda ta auka masa yayin da yake rangadin kifi a ruwan kogi.
Mummunan harin ya faru ne a ƙauyen Tillo da ke ƙaramar hukumar Yauri da yammacin jiya kamar yadda majiyarmu ta bayyana wa wakilinmu.
Bisa ga hakan Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi ya jajantawa Masarautar Yauri da iyalan Malam Usman Mai-Gadi, wanda ya rasa ransa a wannan hari da Dorina ta kai masa.
An yi jana’izar marigayin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a garin Yauri, tare da shugaban Æ™aramar hukumar Yauri, Hon. Abubakar Shu’aibu.