Babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta kori wata kara da aka shigar inda aka bukaci tsige Abdullahi Umar Ganduje daga matsayin shugaban jam’iyyar APC na kasa.
Wata gamayyar magoya bayan APC daga Arewa ta Tsakiya ne suka shigar da Ganduje, APC da kuma INEC kara.
- Tsohuwa Ta Yi Barazanar Kai Ƙarar Wanda Ya Shirya Gasar Cin Taliya Da Jikanta Ya Lashe
- Har Yanzu KuÉ—in Taimakon Ambaliya Da Borno Ta Samu A Hannunta Bai Kai Biliyan 5 Ba
Kungiyar ta bukaci a haramta nadin da aka yi wa Ganduje saboda hanyar da aka bi wajen nadin ya ci karo da dokokin jam’iyyar.
Mai shari’a Inyang Ekwo ne, ya kori karar bisa dalilai da ya zayyana lokacin da yake yanke hukunci.
Mai shari’a Ekwo a lokacin da yake yanke hukunci, ya ce gamayyar magoya bayan jam’iyyar ba su da hurumin shigar da wannan kara.
Alkalin ya kara da cewa gamayyar kungiyar da ta shigar da karar ba ta yi amfani da hanyoyin cikin gida ba wajen magance matsalar kafin ta kai ga kotu.