Wata tankar mai dauke da fetur ta fashe a yankin Maitama da ke Abuja, a daren ranar Litinin, lamarin da ya jikkata mutane da dama tare da haddasa firgici.
Lamarin ya faru ne a kan titin Shehu Shagari, wanda hakan ya jikkata mutane da dama, ciki har da fasinjojin motar haya.
- Tinubu Ya Fara Shirye-shiryen Yi Wa Gwamnatinsa Garambawul
- Kafa Karamin Rukuni Domin Mayar Da Wani Sashe Saniyar Ware Ba Zai Haifar Da Da Mai Ido Ba
Shaidu sun bayyana cewa wajen da lamarin ya faru ya cika makil, yayin da jami’an agajin gaggawa suka yi sauri zuwa domin kai dauki.
Lamarin ya sanya an sanar da asibitoci da ke kusa da yankin don kai daukin gaggawa.
Wani ma’aikacin kiwon lafiya a Asibitin Gundumar Maitama ya tabbatar da cewa ana kula da wadanda suka jikkata.
“Na ga an kawo su domin ba su kulawar gaggawa.”
Wasu daga cikin wadanda suka tsira sun ce direban tankar ya tsere bayan motar ta kife.
Har yanzu ana ci gaba da bincike kan musabbabin faruwar lamarin.
Bindigar da motar ta yi, ya kuma haddasa cunkoson ababen hawa a yankin, wanda ya kawo tsaikon zirga-zirga.
Hukumomi ba su fitar da wata sanarwa kan adadin wadanda suka jikkata ko kuma mutuwa ba.