Gwamnatin tarayya a karkashin Shugaba Bola Ahmed ta ci gaba da jan kafa wajen aiwatar da afuwar harajin shigo da wasu zababbun kayayyakin abinci tun watannin baya da ta sanar da cewa za ta yi hakan.
Kayan abincin da ya kamata a ce an samu damar shigo da su ba tare wani haraji ko haramcin shigo da su ba, sun hada da shinkafa, dawa, masara, alkama, wake, hatsi, gero na tsawon kwanaki 150 daga ranar 15 ga watan Yuli zuwa 31 ga watan Disamban 2024.
- Jerin Kasurguman ‘Yan Bindiga Da Sojoji Suka Hallaka A Arewa
- Jarumai A Masana’antar Kannywood Sun Jajanta Wa Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Maiduguri
Ministan kudi, Wale Edun shi ne ya sanar da janye harajin shigo da kayan abincin da dage takunkumin shigo da su a watan Yuni a wani yunkurin gwamnati Tinubu na kawo saukin kayan abinci da rage matsin rayuwa da ake fuskanta.
A watan Yuli na 2024, Kwanturola Janar na Hukumar Kwastam, Bashir Adewale Adeniyi, ya tabbatar da aniyar gwamnati na aiwatar da umarnin janye takunkumin shigo da kayan abincin.
Rahotonni sun ce duk da rahotan hukumar kididdiga (NBS) na watan Yuli da Agusta da suka nuna cewa hauhawar farashin ya kasance daga kaso 39.53 da kaso 37.52 cikin 100, tsadar kayan abinci a kasuwanni na nan a kan tsadarsa sai ma abun da ya karu.
A wani ziyarar kasuwanni da aka gudanar a ranar Litinin, ya nuna cewa buhun shinkafar mai nauyin kilogram 50 ya kan kasance daga naira 87,000 zuwa naira 106,000. Buhun wake 50kg kuwa ana sayar da shi ne kan naira 65,000 zuwa naira 100,000. ‘Yan Nijeriya da dama ba su iya samun damar cin abinci sau uku a rana, inda suka rage yawan cin abinci sakamakon tsadar rayuwa duk kuwa da cewa an janye harajin shigo da wasu kayan abinci.
Da yake magana kan wannan lamarin a ranar Litinin, babban daraktan cibiyar inganta harkokin ‘yan kasuwa masu zaman kansu (CPPE), Muda Yusuf, ya ce, babban matsalar da ke janyo tsadar kayan abincin shi ne, jan kafar aiwatar da cire harajin shigo da kayan abincin.
A cewarsa, akwai babbar matsala tsakanin sanar da wani shiri da aiwatar da shiri a wannan gwamnati, wanda kuma bai kamata ake samun irin wannan matsalar ba.
Ya tabbatar da cewa daga kafa ga shigo da kayayyakin abincin bai samu aiwatarwa yadda ya dace ba, don haka ne ake samun karin matsala ga tattalin arziki na kasar.
Yusuf ya bukaci gwamnati ta tashi tsaye ta aiwatar da wannan shirin nata domin a samu saukin matsin rayuwa da tsadar kayayyakin abinci da jama’a ke fuskanta a halin yanzun.
Shi ma nasa bangaren, Olufemi Kayode, mamba a kungiyar samar da lasisi na kwastam a Nijeriya (ANLCA), ya ce, har yanzu babu cikakken tsarin janye harajin shigo da kayayyakin.
Ya nuna cewa akwai matsala a tsakanin tsarin sanarwar janyewar da kuma manufar aiwatar da shirin daga wajen kwastam. Don haka ne ya nuna cewa akwai bukatar daga ma’aikatar kudi da kwastam da su samar da manufa ta yadda za a aiwatar da janye harajin domin shigo da kayayyakin ba tare da wani kalubale ba.