Babbar Kotun Tarayya da ke Jihar Kano ta yi watsi da bukatar jam’iyyar APC, na hana Hukumar Zaɓen Mai Zaman Kanta ta Jihar Kano (KANSIEC), na gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar.
APC tare da Hon. Aminu Aliyu Tiga ne suka shigar da korafi a gaban kotun, suna neman umarni don hana KANSIEC ci gaba da shirye-shiryen zaben.
- An Kwantar Da Tsohon Shugaban Sudan Omar al-Bashir A Asibiti
- Majalisa Ta Tabbatar Da Nadin Kudirat A Matsayin Alkalin Alkalan Nijeriya
Haka kuma, sun nemi kotu ta tabbatar da matsayin da kowa ke ciki har sai an saurari shari’ar.
Amma, a hukuncin da mai shari’a Simon Amobeda ya yanke, kotun ta ki karbar bukatarsu, inda ta umarci a sanar da wadanda ake kara don su bayyana dalilin da ya sa bai kamata a yi zaben ba.
Wadanda ake kara sun hada da KANSIEC, shugabanta Farfesa Sani Lawal Malumfashi, Majalisar Dokokin Jihar Kano, Babban Lauyan Jihar, ‘yansanda, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Hukumar Tsaro ta DSS, Hukumar Tsaro ta (NSCDC), da wasu.
Mai shari’a Amobeda ya yi watsi da bukatun APC, tare da bayar da umarnin a gaggauta sauraren shari’ar.
Za a ci gaba da sauraron shari’ar a ranar 4 ga watan Oktoba, 2024.
Haka kuma, alkalin ya gargadi dukkanin bangarorin da su guji yin wani abu da zai iya shafar sakamakon shari’ar.
Tun da farko, KANSIEC ta samu umarnin kotu da ya hana APC da sauran jam’iyyu 18 tsoma baki a harkar zaben, wanda aka tsara zai gudanaa a ranar 26 ga watan Oktoba, 2024.