Gwamnatin Amurka ta jaddada niyyar ta na tallafa wa ‘yan kasuwa mata a Nijeriya domin kai wa ga babban matakin tattalin arziki, domin samar da daidaito, tsaro da kuma ci gaba ga kowa da kowa.
Kasar Amurkan ta ce, wannan tallafin zai zo ne ta hanyar tsangayar ta na Yan Kasuwa mata. Ta bayyana hakan ne a wajen wani taro na kwana uku na tsaffin daliban tsangayar dari da hamsin domin zurfafa ilimin su na fasahar zamani a birnin Legas.
- Babban Taron Samar Da Kayayyaki Na 2024 Ya Sa Kaimi Ga Kulla Ayyukan Hadin Gwiwa 718
- Jan Kafar Tinubu Na Cire Harajin Shigo Da Abinci Na Ci Gaba Da Ta’azzara rayuwa
Shirin zai maida hankali ne wajen saita tsaffin daliban a kan gaba a fannin fasahar zamani, domin kawo kirkire-kirkire da kuma cigaba mai dorewa a harkar kasuwancinsu.
Da yake magana a wajen taron Consul-General din Amurka a Nijeriya, Mr. Will Stebens, ya ce tsangayar ta yan kasuwa mata ta hada sama da mata 130 cikin 150 din da suka kammala karatu a tsangayar a ‘yan shekarun da suka wuce.
“Mun dade muna yin wannan a yan shekarun da suka gabata tun 2019. Wannan shiri wanda gwamnatin Amurka ta dauki nauyi domin koyar da mata masu kananan sana’o’i kuma a taimaka masu wajen inganta kasuwancinsu domin su ci gaba ta hanyar fasahar zamani, noma da kuma tattalin arziki”
Mr. Stebens ya kara da cewa; “Zai taimaka masu su hadu da mentors a Amurka a tsangayar kasuwanci na Arizona da kuma mentors masu zaman kansu kasar Amurka da kuma a tsakanin su. Wadannan matan da suka fito daga sassa a Nijeriya suna taimaka ma juna wajen habbaka kasuwancinsu da kuma samar da ayyuka ga yan Nijeriya”
Ya kuma kara da cewa abu ne mai matukar karfafawa ganin mata na fuskantar kalubalen kasuwanci da kuma hadin gwiwa da kasar Amurka.
Mr. Steben ya kuma ce duk shekara tsangayar tana daukar matan da suka nuna sha’awar shiga makarantar guda 30 zuwa 50 domin su anfana da wannan tsari.
Stebens ya kuma bayyana yadda tsarin yake cigaba da taka rawar gani wajen tallafa wa ‘yan kasuwa mata a Nijeriya ta hanyar tallafa masu da muhimman jarin kasuwanci.
Gwamnatin Tarayya Ta Nemi Tallafin Kasar Rasha Don Kammala Kamfanin Mulmula Karafuna Na Ajakuta.
Gwamnatin tarayya ta sanya hannu a wata yarjejeniya da masu gina kamfanin mulmula karafuna na Ajakuta, Messrs Tyazhapromedport, domin ingantawa, kammalawa da kuma fara aikin kamfanin mulmula karfe a Nijeriya.
Babban ministan harkokin karafuna, Shuaibu Audu, ya sanya hannu a yarjejeniyar a madadin gwamnatin tarayya a birnin Moscow, a wata sanarwa da mai magana da yawun ministan ya fitar, Salamotu Jibaniya a ranar juma’a.
Kamar yadda ta bayyana, an sanya hannu a yarjejeniyar ne lokacin da ministan ya jagoranci tawagar Nijeriya zuwa birnin Moscow a kasar Rasha, daga ranar 14 zuwa 21 ga watan Satumba.
An samar da Kanfanin na Ajakuta ne a shekarar 1979, domin samar da Metallurgical Process Plant tare da Engineering compled da kuma sauran ayyuka makamantansu.
Kamfanin dai ya yi shekaru ba tare da ya sarrafa ko karfe kwara daya ba sakamakon cin hanci da kuma tirka tirkar Shari’a.
An samar da kamfanin ne domin samar da ayyukan kamfani mabanbanta da kuma ayyukan tattalin arziki wanda suke da muhimmanci wajen raba kafa a harkar tattalin arzikin Nijeriya zuwa industry.
Tun bayan zaman shi minista, ministan ya jaddada wa yan Nijeriya cewa kamfanin karfen zai fara aikin sarrafa karafuna domin kawo karshen shigo da karfe daga kasar waje.
Domin tabbatar da wannan buri, kwararrun masana daga Messrs TPE sun ziyarci kanfanin da kuma wajen hako karafuna a garin Irakpe domin fara duba yanayin wajen a watan Agusta, wanda hakan ya yi sanadiyar samun gayyata domin sanya hannu a yarjejeniyar.
Kamfanin Nobostal M and Proforce, wanda na karkashin kanfanin Tyazhpromedport’s consortium suma suna cikin yarjejeniyar.
A wata sanarwa, wakilan na Nijeriya sun duba kayan aikin Messrs Nobostal M, wanda yake a Balakobo a yankin Saratob a kasar Rasha.
Da yake magana dangane da wannan ci gaba, Minista Audu ya ce yarjejeniyar wani babban hanya ne na samar da cigaba mai dorewa a harkar tattalin arzikin Nijeriya.
Ya kuma kara da cewa; “Dawo da kanfanin zai rage shigo da karfe Nijeriya wanda ya kai kusan kimanin dala biliyan hudu a duk shekara kuma zai taimaka wajen tattalin kudaden kasar waje”
A nashi bangaren, sakataren ministan, Chris Isokpunwu, ya ce Nijeriya a shirye take wajen dawo da kanfanin Ajakuta da kuma NIOMCO.
A nashi batun, wakilin kasar Rasha ya jaddada cewa za su yi kokari wajen ganin cewa sun girmama yarjejeniyar daidai da yadda gwamnatin Nijeriya ta bukata.