A bana aka cika shekaru 95 da kafuwar rundunar sojan ‘yantar jama’ar kasar Sin. A shekarun baya, sojojin kasar Sin sun kasance a matsayin ginshikan kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.
Sojoji 413 da kasar Sin ta tura zuwa kasar Mali karo na 8 domin kiyaye zaman lafiya, sun samu lambar yabon zaman lafiya ta MDD saboda ficen da suka yi wajen tabbatar da tsaro, yin sintiri, ayyukan gine-gine da kiwon lafiya.
Laftana janar Carlos Humberto Loitey, mashawarcin MDD a fannin aikin soja ya bayyana cewa, “Na shafe shekaru 4 da rabi ina rike da mukamin mashawarcin MDD a fannin aikin soja. Gudummawar da sojojin kasar Sin suka bayar wajen gudanar da aikin kiyaye zaman lafiya karkshin laimar MDD, ta burge ni sosai.
Kasar Sin ta aika da ma’aikatan kiyaye zaman lafiya kusan dubu 2 da dari 5 domin gudanar da ayyukan zaman lafiya guda 8 cikin ayyuka 12. Don haka kasar Sin tana kan gaba a duniya wajen ba da gudummawar tabbatar da zaman lafiya.
Ta karfafa muhimmin karfin MDD na kiyaye zaman lafiya.”
A shekaru fiye da 30 da suka wuce, sojojin kasar Sin masu aikin kiyaye zaman lafiya, sun ba da muhimmiyar gudummawa wajen daidaita sabani cikin ruwan sanyi, kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a shiyoyi da kara azama kan ci gaban kasashen da aka tura su. (Tasallah Yuan)