Gwamnatin Jihar Kano ta shirya taron ƙara wa juna sani a wani ɓangare na bukukuwan cikar ƙasar nan shekara 64 da samun ‘yancin kai.
Taron wanda ya mayar da hankali kan irin ci gaban da aka samu da ƙalubalen da ke addabar ƙasar nan, ya gudana ne a ɗakin taro na fadar Gwamnatin Kano (Coronation Hall).
Da yake jawabi, Gwamnan Jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya taɓo batutuwa masu motsa zuciya, inda ya bayyana cewa bisa sake fasalin shugabanci da tabbatar da riƙon amana, Jihar Kano ta zama madubi ga jihohi da kuma fagen ci gaban siyasar ƙasar nan.
Gwamna Abba Kabir Yusuf bayan jinjina wa ƙoƙarin kwamitin da ya tsara wannan taro wanda ya ce ya yi kyakkyanwan hange da tunanin zaƙulo masu gabatar da jawabai waɗanda suka kasance mutane masu kima da daraja, ya yi ƙarin haske kan kyakkyawan salon shugabancin gwamnatinsa.
Ya ce gwamnatin ta mayar da hankali sosai kan wasu muhimman ayyuka da suke da alaƙa da kyautata rayuwar al’ummar Jihar Kano kai-tsaye.
“Zan yi amfani da wannan dama domin bayyana wasu daga cikin manyan nasarorin da Gwamnatin Kano ta samu a ɓangarori daban-daban, wannan kuma wani ƙoƙari ne na magance ƙalubalen da ya jima yana addabar rayuwar mazauna Kano.
‘A ɓangaren ilimi mun samu gagarumar nasarar sake farfaɗo da sashin, hakan ya haɗa da ginawa tare da gyaran makarantu, ɗaukar ƙwararrun malamai, samar da kayan koyo da koyarwa, haka kuma mun bujiro da tsarilimantarwa ta hanyar fasahar zamani da koyar da sana’o’i ga matasa.
“Sashin lafiya na cikin ɓangarorin da wannan gwamnati ke bai wa kulawa ta musamman, ta yadda aka ɗaga darajar cibiyoyin kiwon lafiya, da kyautata tsarin kula da lafiyar mata masu ciki da yara ƙanana, kana an kuma yi duk mai yiwuwa wajen ganin ba a bar jama’ar karkara a baya ba. Sai kuma yadda muka tunkari ƙalubalen cututtuka kamar maleriya, ƙarancin abinci mai gina jiki da sauran cututtukaka masu yaɗuwa.”
Har ila yau, Gwamna Abba Kabir ya nunar da cewa, sauran ɓangarorin da ke samun kyakkyawar kulawa a gwamnatinsa sun haɗa da sashin noma, Tsaro, Tallafa wa matasa da jari iri daban-daban, inganta tsarin aikin gwamnati da bayar da fifiko wajen biyan basussukan kuɗaɗen fansho da aka danne wa masu su tsawon lokaci.
Gwamnan ya kuma bayyana irin gagarumar nasarar da suka samu ta fuskar manyan ayyuka kamar kyautata muhalli, inganta harkar wasanni waɗanda suka samar wa Jihar Kano gagarumin ci gaba.
Daganan sai Gwamna Abba Kabir ya jaddada buƙatar haɗin kai a tsakanin al’ummar Jihar Kano domin ƙara samun nasarar da ake fata, yana mai cewar, “wannan kuma bai zai samu ba sai ta hanyar jajircewa, sadaukar da kai domin kare kimar al’ummar mu.” In ji shi.