Kungiyar ‘Yan jarida ta Nijeriya (NUJ) reshen jihar Kebbi, ta taya Gwamna Nasir Idris murnar cikar Nijeriya Shekaru 64 da samun ‘yancin kai.
A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun shugaban kungiyar, Kwamared Garba Muhammad Yeldu da Sakatare Abubakar Attahiru, NUJ ta amince da sadaukarwar da shugabanni da jarumai masu kishin kasa suka yi a baya wadanda suka yi fafutukar kwato ‘yancin Nijeriya.
Sun bukaci ’yan Nijeriya musamman mazauna Kebbi da su yi wa shugabanninsu addu’a don bunkasa ci gaba da hadin kai a jihar da kasa baki daya.
NUJ ta yaba wa Gwamnatin Gwamna Idris bisa nasarorin da ta samu a fannin tsaro, ilimi, kiwon lafiya, noma, da kuma tallafa wa Jama’a a cikin shekara ta farko.
Waɗannan nasarorin sun haɗa da ayyukan samar da ababen more rayuwa, shirye-shiryen ƙarfafa wa mata, da tallafi ga manoma.
Kungiyar ta bayyana gamsuwarta ga manufofin Gwamna Idris, inda ta yi hasashen za su daukaka jihar Kebbi nan da shekaru uku masu zuwa.
Sun yi kira ga jama’ar jihar da su mara wa gwamnatin baya wajen cika alkawuran da ta dauka a yakin neman zabe.