Zanga-zanga ta barke kan tabarbarewar tattalin arziki a Nijeriya a Jihar Legas da Babban Birnin Tarayya, Abuja da safiyar ranar Talata.
A Legas, masu zanga-zangar sun taru a karkashin Gadar Ikeja don bayyana bacin ransu kan kalubalen tattalin arzikin da ake fuskanta.
- NUJ Ta Taya Gwamnan Kebbi Da Nijeriya Murnar Cika Shekaru 64 Da Samun ‘Yancin Kai
- Murnar Ƴanci: Gwamna Fintiri Ya Yafe Wa Fursunoni Biyu
Omoyele Sowore, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar African Action Congress (AAC) a zaben 2023, ya jagoranci zanga-zangar a Legas, a cibiyar kasuwanci ta Nijeriya.
Kungiyoyin fararen hula daban-daban ne suka shirya zanga-zangar ta #EndBadGovernance.
Zanga-zangar ta mayar da hankali kan batutuwan da suka hada da hauhawar farashin man fetur, tsadar kayan abinci, da kuma yadda hauhawar farashi ke shafar rayuwar yau da kullum ta ‘yan Nijeriya.
Zanga-zangar ta gudana ne yayin da ake bikin cika shekaru 64 da samun ‘yancin kai na Nijeriya, bayan zanga-zangar #EndBadGovernance da aka gudanar a duk fadin kasar daga 1 zuwa 10 ga watan Agusta, wadda ya rikide zuwa tashin hankali a wasu jihohin Nijeriya.
A Abuja ma, masu zanga-zangar sun fito suna bayyana damuwarsu kan tabarbarewar tattalin arzikin kasar.
Amma, jami’an tsaro sun kafa shingaye a manyan hanyoyin zuwa filin Eagle Square, inda ake gudanar da bukukuwancikar Nijeriya shekaru 64 da samun ‘yancin kai.
Wannan zanga-zangar na nuna yadda ‘yan kasa ke nuna rashin jin dadinsu kan manufofin tattalin arziki da gwamnati ke aiwatarwa karkashin jagorancin shugaban kasa Bola Tinubu.
Jama’a na bukatar gwamnati ta dauki matakin gaggawa don saukaka musu wahalhalun rayuwa.
Ga hotunan yadda zanga-zangar ta gudana: