Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya ce idan har shugabar majalissar wakilan Amurka Nancy Pelosi ta ziyarci yankin Taiwan, Sin za ta dauki hakan a matsayin babban mataki na tsoma baki cikin harkokin gidan ta, kuma rundunar sojojin ‘yantar da al’umma ta Sin ba za ta zuba ido kawai ba.
Zhao ya yi wannan gargadi ne a Litinin din nan yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, lokacin da wani dan jarida ya yi masa tambaya don gane da shirin Pelosi, na gudanar da ziyara a wasu sassan nahiyar Asiya.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin ya kara da cewa, tabbas Sin za ta aiwatar da tsauraran matakai masu karfi, na tunkarar wannan kalubale, tare da kare ikon ta na mulkin kai da tsaron martabar yankunan ta. (Mai fassarawa: Saminu Alhassan daga CMG Hausa)