Tsohon Gwamnan Jihar Taraba, Arch Darius Ishaku, ya samu belin Naira miliyan 150 daga babbar kotun tarayya dangane da zargin zambar da ake masa na Naira biliyan 27.
Mai Shari’a Sylvanus Oriji, wanda ya jagoranci shari’ar, ya umarci cewa Ishaku ya kawo mutane biyu da za su tsaya masa, kowannensu ya kasance da kadarar da ta kai wannan adadi, ɗaya daga cikinsu ya kasance darekta a aikin gwamnati, kuma dukkansu mazaunan Abuja.
- Gwamnatin Tarayya Za Ta Gina Wa Alkalai Gidaje 40 A Abuja
- Tsadar Rayuwa: Zanga-zanga Ta Barke A Abuja Da Legas
Bugu da ƙari, kotun ta hana Ishaku da abokin zamansa, Bello Yero, fita ƙasar waje ba tare da izininta ba. Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), wadda ta kawo ƙarar, ba ta yi tirjiya da roƙon beli ba saboda Ishaku ya cika sharuddan belin da aka bayar.
Ishaku, wanda ya yi wa’adin shekaru takwas a matsayin gwamna har zuwa 2023, yana fuskantar tuhuma 15 kan karkatar da kudade daga hukumar ƙananan hukumomi da harkokin Sarakunan Gargajiya. Ya musanta dukkan tuhume-tuhumen, kuma za a fara shari’ar a watan Nuwamba.