Zaunannen wakilin Sin a ofishin MDD dake Geneva da sauran kungiyoyin kasa da kasa a Switzerland, jakada Chen Xu, ya yi jawabi a gun taron duba yanayin hakkin bil’adama da yankunan Falasdinu da sauran kasashen Larabawa da aka mamaye ke ciki karo na 57 na kwamitin kare hakkin dan Adam jiya Laraba, inda ya bayyana matsayin bangaren Sin a kan matsalar Falasdinu.
Chen Xu ya bayyana cewa, matsalar Falasdinu ta kasance har tsawon shekaru 70, wadda ta kawo babban bala’i ga jama’ar Falasdinu. Barkewar rikicin zirin Gaza za ta cika shekara daya, amma yakin na ci gaba da habakawa, kuma an sake tayar da yaki a Lebanon, da wahala a iya aiwatar da “manufar kafa kasashe biyu”.
- Wakilin Sin Ya Bukaci A Kyautata Tsarin Duniya Da Gyara Rashin Adalci Da Aka Yi Wa Afirka
- Ambaliya: Jamus Ta Bai Wa Nijeriya Da Wasu Tallafin Yuro Miliyan 24
Bangaren Sin ya mai da hankali sosai kan yanayin hakkin dan Adam na Falasdinu da sauran kasashen Larabawa, ya dage wajen goyon bayan jama’ar Falasdinu don maido da halaltaccen hakkin al’ummar kasar, kuma ya nuna adawa da zargin dukkan ayyukan da ke halaka fararen hula musamman mata da yara. Bangaren Sin ya yi kira da a tsagaita bude wuta na dogon lokaci cikin gaggawa, da kuma daina dukkan ayyukan dake tsananta rikicin da ma ta’azara halin da yankin ke ciki, ta yadda za a saukaka bala’in jin kai na zirin Gaza.
Bugu da kari, Chen Xu ya jadadda cewa, ya kamata al’ummar kasa da kasa ta aiwatar da kudurin kiyaye hakkin jama’ar Falasdinu na babban taron MDD da kwamitin kare hakkin dan Adam da kuma shawarwarin da abin ya shafa na kotun kasa da kasa, don kare halaltaccen hakkin jama’ar Falasdinu. (Safiyah Ma)