Hukumar Kula da Kwallon Kafa ta Duniya FIFA, ta dakatar da shugaban hukumar kwallon kafar Kamaru, Samuel Eto’o daga zuwa kallon wasannin kasar zuwa watanni shida sakamakon samun sa da laifin karya dokar da’a karo biyu ta FIFA.
An hukunta tsohon dan wasan Barcelona da Chelsea ne sakamakon abin da ya faru a gasar kofin duniya ta matasa ‘‘yan kasa da shekara 20 ranar 11 ga watan Satumba, inda Brazil ta doke Kamaru 3-1 a zagaye na biyu.
Kamar yadda FIFA ta fitar da jawabi, an yi kalamai na batanci da nuna halin rashin da’a daga ‘‘yan wasa da jami’ai a karawar da aka yi a Bogota a Colombia, inda Eto’o ya halarci karawar. Hukuncin yana nufin an hana Eto’o mai shekara 43 a duniya halartar duk wani wasan Kamaru na maza da na mata tun daga masu karancin shekaru zuwa babbar kungiya har wata shida, kuma FIFA ta ce hukuncin ya fara aiki nan take, ta kuma ce ta sanar da Eto’o kan wannan matakin da ta dauka.
Tawagar Kamaru za ta kara da Kenya gida da waje a wasan neman shiga gasar kofin Afirka 2025 da za a yi a Morocco, inda za su kara a cikin watan Oktoba.
A ranar Litinin Eto’o ya ja ragamar taron hukumar kwallon kafar kasar kan tsara yadda za su fuskanci Harambe Stars ranar 11 ga watan Oktoba, amma kuma har yanzu hukumar kwallon kafar Kamaru ba ta ce komai ba kan wannan hukuncin.