• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tinubu Ya Samar Da Naira Biliyan 29 Don Gyara Hanyoyin Kasar Nan

by Abubakar Abba and Sulaiman
1 year ago
Tinubu

A cikin watan Satumbar wannan shekarar, Gwamnatin tarayya ta fitar da sama da Naira biliyan 29, domin a inganta manyan hanyoyin kasar nan, tare da kuma bunkasa hanyoyin ruwa wanda ma’aikayar ayyuka ta tarayya, ke jagoranta.

A cewar wasu bayanai da aka samo a kafar sada zamunta ta gwamnatin, wani kamfanin cikin gida na BudgIT ne, aka bai wa kwangilar aikin.

  • Daga Yanzu Saudiyya Ce Za Ta Kula Da Abincin Alhazan Nijeriya -NAHCON
  • Wakilin Sin: Ya Kamata A Kiyaye Da Karfafa Gudummawar MDD A Fannin Yaki Da Ta’addanci

Wasu daga cikin kudaden da aka fitar sun hada da; Naira biliyan 5.88, da aka bai wa kamfanin Reinforced Global Resources Ltd kwangilar  aikin gyran babbar hanyar  Ugep-Opkosi wacce ta hada da  jihar Koros Ribas da jihar Ebonyi .

LABARAI MASU NASABA

Bayan Shekara 20 Nijeriya Ta Sake Dawo Da Tsarin Bayar Da Hayar Kananan Jiragen Sama

Tashoshin Jiragen Ruwa Sun Samar Da Kashi 19.6 Na Fitar Da Kayan Da Ba Su Shafi Mai Ba—Dantsoho

Kazalika, an kuma bai wa kamfanin JRB Constructions Company Ltd kwangilar  Naira biliyan 4.42 don gyran babbar hanyar Potiskum-Jakusko-Gashua da ke a jihar Yobe.

Kwangilayr yin sabuwar  hanyar   Maraba Donga da ke a jihar Taraba, an baiwa kamfanin  Rockborough DL Prime Ltd Naira biliyan 1.26 don yin aikin, inda kuma aka bai wa kamfanin .Truetech Global Inbestment Serbices Ltd  Naira biliyan 1.25 don yin aikin babbar hanyar Gabas maso yamma da ke a jihar Delta.

Bugu da kari, na kuma bai wa kamfanin HMF Construction Ltd Naira biliyan 1.04 domin ayyukan manya hanya da ban da ban na Abeokuta-Ajebo da ke a jihar Ogun.

A jihar Sokoto kuma, an  bai wa kafanin Sholly Frontlink Impec Ltd Naira biliyan 567.37. don yin aikin manyan hanyoyin Aliero, inda kuma aka bai wa kamfanin  Logine International Ltd, Naira miliyan 780.98 domin yin murafan magudana.

A bangaren aikin samar da ruwa sha kuwa, an ware Naira miliyan 905.24, domin a kammala Dam din Farin Ruwa da ke a karamar hukumar Wamba a jihar  Nasarawa, inda aka bai wa kafanin Wiz China Worldwide Engineering Ltd kwangilar yin aikin.

An kuma kara ware wasu karin Naira miliyan N678.16 a ,matsayin kudin hadaka na wanda yake da kaso 50, na aikin samar da ruwan sha a karkashin Asusun bayar da tallafi na kananan yara na majalisar diinkin duniya.

Bugu da kari, bayanna sun nuna cewa, gwamnatin ta  bai wa kamfanin Medabille Construction Ltd Naira biliyan 1.90 don yin aikin gina wasu sabbin sakarariya  a jihar Kebbi tare da kuma bai wa kamfanin Candon Construction Ltd, Naira biliyan 1.82 don gina sakatariya ta tarayya a  jihar Abia tare da kuma bai wa kamfanin Strabic Construction Ltd, Naira biliyan1.82 don gina wata sakatriyar a jihar  to Ebonyi.

An kuma bai wa kamfanin Steady Lane Nigeria Ltd Naira biliyan 1.49 don gina sakatariya a garin  Lokoja da ke a jihar Kogi.

Sauran ayyukan gyran manyan hanyoyin, an bai wa kamfanin Rockborough DL Prime Ltd Naira biliyan 1.23, don gyran babbar hanyar Zamfara, an kuma bai wa kamfanin Gerawa Global Engineering Ltd Naira miliyan 596.36 a matsayin kafin Alkami na aikin babbar hanyar jihar  Borno, inda kuma aka bai wa kamfanin  Anbez Innobations Ltd, Naira miliyan 511.07 domin gyran babbar hanyar Katsina zuwa Daura.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Bayan Shekara 20 Nijeriya Ta Sake Dawo Da Tsarin Bayar Da Hayar Kananan Jiragen Sama
Tattalin Arziki

Bayan Shekara 20 Nijeriya Ta Sake Dawo Da Tsarin Bayar Da Hayar Kananan Jiragen Sama

October 3, 2025
Tashoshin Jiragen Ruwa Sun Samar Da Kashi 19.6 Na Fitar Da Kayan Da Ba Su Shafi Mai Ba—Dantsoho
Tattalin Arziki

Tashoshin Jiragen Ruwa Sun Samar Da Kashi 19.6 Na Fitar Da Kayan Da Ba Su Shafi Mai Ba—Dantsoho

October 3, 2025
Majalisar Wakilai Za Ta Sasanta Dangote Da NUPENG
Tattalin Arziki

Majalisar Wakilai Za Ta Sasanta Dangote Da NUPENG

September 27, 2025
Next Post
Sin Na Goyon Bayan Gaggauta Aiwatar Da Shawarar Cimma Gajiya Daga Fasahohin Dijital

Sin Na Goyon Bayan Gaggauta Aiwatar Da Shawarar Cimma Gajiya Daga Fasahohin Dijital

LABARAI MASU NASABA

TCN

Jami’an Tsaro Sun Cafke Ɓarayin Kayayyakin Turakun Wutar Lantarki Na Hanyar Mando Zuwa Jos

October 9, 2025
An Yi Tafiye-tafiye Miliyan 16.34 Da Suka Shafi Shiga Da Fita Daga Kasar Sin Yayin Hutun Kwanaki 8 Na Kasar 

An Yi Tafiye-tafiye Miliyan 16.34 Da Suka Shafi Shiga Da Fita Daga Kasar Sin Yayin Hutun Kwanaki 8 Na Kasar 

October 9, 2025
Nijeriya Ta Yi Asarar Ganga Miliyan 13.5 Na Ɗanyen Mai Ta Hanyar Sata Da Zagon-ƙasa – NEITI

Nijeriya Ta Yi Asarar Ganga Miliyan 13.5 Na Ɗanyen Mai Ta Hanyar Sata Da Zagon-ƙasa – NEITI

October 9, 2025
Duniya Ta Kara Ganin Bunkasuwar Sin a Lokacin Hutun Murnar Ranar Kafuwar Sabuwar Kasar

Duniya Ta Kara Ganin Bunkasuwar Sin a Lokacin Hutun Murnar Ranar Kafuwar Sabuwar Kasar

October 9, 2025
Fursunoni Ba Za Su Samu Damar Kada Kuri’a Ba A Zaben 2023 – INEC

Batun Umarnin Kotu Na Kama Tsohon Shugaban INEC Ƙage Ne Kawai – Shugaban Jam’iyyar AA 

October 9, 2025
An Samu Karuwar Sayayya Yayin Hutun Bikin Kafuwar Kasar Sin

An Samu Karuwar Sayayya Yayin Hutun Bikin Kafuwar Kasar Sin

October 9, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC 

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC 

October 9, 2025
Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26

Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26

October 9, 2025
SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati

SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati

October 9, 2025
An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba

An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba

October 9, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.