Gwamna Babagana Zulum ya gabatar da ƙarin kasafin kuɗi na Naira biliyan 61 ga Majalisar Dokokin Jihar Borno don magance lalacewar gine-ginen da ambaliyar ruwa mai tsanani ta haifar a jihar.
Sabon kasafin kuɗin na neman gyara kasafin kuɗin Naira biliyan 358.7 da aka amince da shi a watan Janairu, inda zai ƙaru zuwa jimillar Naira biliyan 419.7.
- Hare-haren ‘Yan Bindiga A Sahel Sun Jefa Shugabannin Soji Cikin Zulumi
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 4, Tare Da Kwato Makamai A Borno
Wannan ƙarin kasafin kuɗi zai mayar da hankali ne wajen sake gina manyan tituna, da gadoji, da asibitoci, da samar da agaji ga manoma da sauran waɗanda annobar ta shafa.
Ambaliyar ruwa ta watan Satumbar 2024 ta raba mutane kimanin miliyan biyu da muhallansu, ta kuma lalata gidaje 200,000 tare da haifar da mummunar ɓarna a Maiduguri da kewaye.
Kakakin Majalisa, Abdulkarim Lawan, ya nuna buƙatar ɗaukar mataki nan da nan, tare da yabawa ƙoƙarin ƙungiyoyin cikin gida da na ƙasa da ƙasa, ma’aikatan lafiya, da hukumomin tsaro a taimakon waɗanda ambaliyar ta shafa. Ziyarorin Gwamna Zulum na duba yankunan da abin ya shafa sun nuna gaggawar ɗaukar mataki a jihar.