Masana harkokin lafiyar abinci, sun bayyana amfanin da ganyen zogale ke da shi a jikin Dan’adam, sakamakon sinadarin da yake kunshe da su.
Har ila yau, bincike ya tabbatar da cewa; zogale itace ne mai matukar albarka, domin kuwa ya kan fito har a wurin da babu ruwa.
Don haka, ganyensa da sassakensa; na da matukar amfani a jikin mutum. Sannan kuma, yana da dauke da sinadarin A.B.C.D har ma da E, kana kuma yana dauke da sinadarin calcium da potassium, kana kuma mansa yana cikin mayukan da suka fi tsada a duniya.
Kazalika, akwai magunguna 18 da zogale ke yi ga lafiyar Dan’adam kamar haka:
– Ana dafa ganyen zogale da zuma a sha kamar shayi, domin maganin Olsa (Ulcer).
– Ana kuma shafa danyen ganyen zogale a kan goshi, don maganin ciwon kai.
– Haka nan, ga wanda ya ji wani rauni ko sara; idan ya shafa danyen ganyen zogale, jinin zai tsaya nan take da izinin Allah.
– Ga mai fama da kurajen jiki, sai ya hada garin zogale da man zaitun; ya rika shawa.
– Ana kuma zuba garin zogale a kan gyambo ko wani rauni, domin ya yi saurin warke.
– Sanya garin zogale a cikin abinci, na maganin hawan jini da kuma kara wa mutum kuzari,
– Ana dafa ganyen zogale, a saka kanwa ‘yar kadan; don maganin shawara.
– Ga mai fama da ciwon ido, zai rika diga ruwan danyen zogale; haka nan shi mai fama da ciwon kunne.
– Macen da ke shayarwa kuma, ta dafa furen zogale da zuma; domin samun karin yawan ruwan nono.
– Wanda ke fama da yawan fitsari ko ciwon Siga, sai ya rika shan furen zogale da citta kamar shayi.
– Kazalika, cin zogalen ma a haka; na maganin tsutsar ciki, musamman ga yara.
– Ana daka ganyen zogale da ‘ya’yan baure a sha da nono ko kunu, domin kuwa yana maganin ciwon hanta.
– Ga mai fama da sanyin kashi ko wani kumburi, sai ya soya ‘ya’yan zogale ya daka su; ya kuma hada da man kwakwa (man- ja) sai ya rika shafawa.
– A daka zangarniyar zogale da ‘ya’yan da ke ciki da kaninfari, citta, masoro da kuma kimba, domin karin karfin namiji, sannan yana kara wa mata nishadi.
– A daka saiwar zogale da ‘ya’yan kankana a sha a nono, yana maganin tsakuwar ciki (Apendis).
– Haka nan, yana maganin typhoid, maleriya, basir da shawara; ta hanyar yawan shan ruwan dafaffen zogale.
– Kazalika, zogale na rage radadin ciwon HIB ta hanyar shan dafaffen ruwan zogalen.