Kamfanin Swakop na hakar Uranium mai jarin kasar Sin dake aiki a Namibia, ya tallafawa kokarin gwamnatin kasar na cike gibin da take fuskanta na kayayyakin dijital ta hanyar bayar da gudunmuwar kumfutoci ga makarantar Lazarus Haufiku na kauyen Oshamba dake arewacin yankin Ohangwena.
Kimanin dalibai 550 ne za su ci gajiyar gudunmuwar da ta hada da kumfutoci 16 da wata na’urar buga rubuta wato Printer, tare da katange makarantar domin tabbatar da tsaro.
- Ana Shirin Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 18 Ta Jiragen Kasa A Kasar Sin A Yau Lahadi
- Yadda Na Kirkiro ‘Brain-chip’ Da Ke Dawo Wa Wadanda Aka Haifa Da Makanta Ganinsu – Elon Musk
Yayin bikin mika gudunmuwar, wanda ya samu halartar jami’an gwamnati da mutanen kauyen, ministar kula da raya ilimi da fasaha da al’adu ta kasar Ester Nghipondoke, ta ce wannan gudunmuwa alama ce mai karfi dake nuna muhimmancin ilimi.
Ta ce gangamin zuba jari ga bangaren ilimi na kamfanin Swakop, yana karfafa gwiwa, inda ta ce cikin shekarar 2024 kadai, ya zuba sama da dalar Namibia miliyan 3, kwatankwacin dalar Amurka 172,000 a fadin yankunan kasar, tana mai cewa, tallafin kamfanin ya nuna muhimmancin da ake ba bangaren ilimi. Ta kara da cewa, yayin da Namibia ke kokarin karkata ga amfani da na’urori masu kwakwalwa, abu ne mai muhimmanci makarantu su samu kayayyakin da albarktun da ake bukata domin samun kyakkyawar makoma. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)