Bisa alkaluman da ma’aikatar kula da masana’antu da fasahar sadarwa ta Sin ta fitar, daga watan Janairu zuwa Agustan wannan shekara, masana’antar samar da kayayyakin sadarwa na laturoni ta Sin ta bunkasa cikin sauri, sannan kuma ana ci gaba da samun karuwar fitar da kayayyakin zuwa kasashen waje.
Bayanan sun nuna cewa, a cikin watanni takwas na farkon bana, darajar masana’antun samar da kayayyakin sadarwa na laturoni masu babban ma’auni ta karu da kashi 13.1 cikin dari bisa makamancin lokacin a bara. Daga cikin manyan samfuran, yawan wayoyin salula da aka samar ya kai biliyan 1.015, yawan kananan kamfuta na Lap-top da wayoyin salula da aka fitar ketare, sun karu da kashi 2.0 cikin dari da kashi 4.6 cikin dari bisa makamancin lokacin a shekara.
Bugu da kari, jarin da aka zuba a masana’antar samar da kayayyakin sadarwa na laturoni na bisa daidaitaccen matsayi, kuma jarin dindindin da aka zuba ya karu da kashi 14.2 cikin dari idan aka kwatanta da na bara.(Safiyah Ma)