Kasar Sin ta yi Allah wadai da harin ta’addancin da aka kai a Pakistan, wanda ya yi sanadin mutuwar Sinawa biyu da ma wasu ‘yan kasar Pakistan. Haka kuma ta jajantawa wadanda suka jikkata, da ma iyalan wadanda suka rasa rayukansu.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin ne ya bayyana haka a yau, lokacin da yake amsa tambaya game da harin da aka kai wa motocin wani kamfanin kasar Sin a Pakistan, a jiya Lahadi.
- Darajar Masana’antun Samar Da Kayayyakin Sadarwa Na Laturoni Ta Sin Ta Karu Da 13.1% A Watanni Takwas Na Farkon Bana
- Shugabannin Sin Da Korea Ta Arewa Sun Taya Juna Murnar Cikar Dangantakar Diplomasiyyar Kasashensu Shekaru 75 Da Kulluwa
A cewar kakakin, Sin na bukatar Pakistan ta yi dukkan kokarin da ya kamata domin jinyar wadanda suka jikkata tare da aiwatar da cikakken bincike don kama wadanda ke da hannu da kuma tabbatar da sun fuskanci fushin doka.
Ya kara da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da goyon bayan Pakistan wajen inganta ayyukan yaki da ta’addanci, kuma a shirye take ta hada hannu da Pakistan din wajen dakile duk wani yunkuri na lalata dangantakar dake tsakaninsu.
Kafin wannan, rahotanni sun nuna cewa, wani harin ta’addanci a birnin Karachi mai tashar ruwa a kasar Pakistan, ya yi sanadin mutuwar Sinawa biyu da jikkatar wani guda, baya ga ‘yan kasar Pakistan da dama da suka mutu da kuma jikkata sanadin harin na jiya Lahadi da dare.
Ofishin jakadancin Sin ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa, inda ya kara da cewa, harin ya auku da misalin karfe 11 na dare a jiya Lahadi, lokacin da ‘yan ta’adda da suka kai hari kan jerin gwanon motoci daga kamfanin tashar lantarki ta Qasim a kusa da filin jirgin saman kasa da kasa na Jinnah na birnin Karachi, fadar mulkin lardin Sindh dake kudancin kasar Pakistan.
Gobarar da ta tashi bayan fashewar wani abu a jiyan, ta kuma shafi motoci da dama a kusa da filin jirgin na Karachi. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)