Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mika gaisuwar ban girma ga dattawa a jajibirin Ranar Tsofaffin Kasar, wadda a bana ta fado ranar Juma’a.
Xi ya bayyana fatan cewa, dattawa za su samu kulawa mai kyau, su ji dadin rayuwarsu, su kuma ci gaba da cika burikansu.
Xi ya bayyana hakan ne a cikin wasikar da ya aike wa wakilan tsofaffi na cikin shirin sa kai na kasar. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp