Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya sake jaddada aniyarsa na tabbatar da kokarinsa na aminci da ingancin tsarin hada-hadar kudade a Nijeriya.Â
CBN ya bayar da wannan tabbacin ne domin tabbatar wa kwastomomi cewa ba su da wani abu na firgici kan kariyar kudadensu, bankin ya nanata cewa, dukkanin masu ajiyar kudade a bankunan Nijeriya, kudadensu na cikin kariya da aminci.
- Janar Gowon: Tsohon Shugaban Kasa Mafi Tsawon Rai A Nijeriya Na Cika Shekara 90
- Babu Hannun Mijina A Wahalar Da Ƴan Nijeriya Ke Sha
Tabbacin na zuwa ne a daidai lokacin da jama’a suka shiga firgicin rugujewar wani daga cikin manyan bankunan da suke Nijeriya.
An gano wani faifaiyin bidiyo a soshal midiya, inda wasu kwastomomi ke kokawa kan yadda bankinsu ya kasa ba su damar yin huldar cire kudade ta hanar gizo ko kuma a zahirance, inda suke zauna a jikin bankin jangwan-jangwan suna ta kokawa.
Sabanin fargabar, CBN ya ba da tabbacin cewa kafin a kafa kowace banki akwai ka’idoji da dokokin da ake bi wajen ganin an kiyaye dokiyar jama’an da suke hulda da kowani banki domin kare hada-hadar kudadensu.
A wata sanarwar da bankin ya fitar a ranar Talata dauke da sanya hannun kakakinsa, Hakama Ali, na cewa, “Ana gudanar da gwajin gano karfin kowace banki da nufin gano karfin cibiyoyin kudinmu.”
Babban bankin ya ce ya gabatar da gargadi kan kowace tsari da ya zama na tafiya yadda ya kamata domin magance kowace irin barazana da shawo kansu bayan gano matsala, ta yadda za a samu hanyoyin magance matsalar a kan kari.