Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP), Farfesa Pat Utomi, ya janye daga takarar 2023.
Utomi ya ce ya janye wa sabon dan jam’iyyar kuma tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi.
- Okorocha Ya Musanta Zargin Damfarar N2.9bn, Zai Ci Gaba Da Zama A Hannun EFCC
- Zaben Fidda Gwani Na PDP: Wike Shi Ne Wanda Ya Yi Nasara —Orji Kalu
Utomi yayi magana ne a Asaba, babban birnin jihar Delta a babban taron jam’iyyar LP da ke gudana a yau litinin.
Gaba dayan wurin taron dai ya barke da murna tare da jinjinawa a daidai lokacin da Farfesa Utomi ya sanar da cewa ya ajiye mukaminsa na Obi.
Ku tuna cewa Obi ya fice daga jam’iyyar PDP ya koma jam’iyyar Labour bayan (NCFront) ta amince da jam’iyyar a matsayin babbar jam’iyyar ta uku da za a kara da ita a zaben 2023.
NCFront dai ita ce babbar kungiyar wadda ta bayyana kanta a matsayinta kan jam’iyyun (APC) mai mulki da kuma PDP.
Tana fatan hada karfi da karfe da matasan Najeriya domin kawar da mamayar manyan jam’iyyun siyasa biyu.